Nijeriya warki ce daidai ƙugun kowa – Fani Kayode kan barazanar kutsen Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode ya ci alwashin cewa ƴan Nijeriya za su iya jure wa dukkan wani barazanar soja da Amurka ke shirin ɗauka akan ƙasar bayan Shugaba Donald Trump ya umarci a fara shirin kai farmaki.

A wani rubutu ta kafar X ranar Lahadi, Fani-Kayode ya yi alla-wadai da kalaman Trump yana mai bayyana shi a matsayin ‘azzalumin shugaba’ da ke yi wa Nijeriya barazana da tashin-tashina da mamaya.

Tsohon ministan ya ce wani aboki ya koka game da kalaman Trump, yana mai jaddada cewa ƴan Nijeriya ba za su gudu su bat ƙasarsu ba, za su tsaya wajen kare ta matuƙar Amurka ta ƙaddamar da hari akanta.

Fani-Kayode ya kuma zargi Trump da ɗaukar matsaya biyu, inda ya zarge shi da kawar da kai akan abinda ake yi na kisan kiyashi a Sudan da Isra’ila yayin da yake yi Nijeriya ganin ƙasar da ake tauye ƴancin wani addini.

Kalaman Donald Trump sun yamutsa hazo a kafafen sadarwa ganin yadda masana harkar siyasa da difulomasiyya ke gargaɗin hakan ka iya haifar da koma-baya ga harkokin ƙasa-da-ƙasa da zaman lafiya.

By Babaji