
Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɓarawon mota ya yi nasarar kutsawa cikin Gidan Gwamnatin jihar Kano da asubahin ranar Litinin, inda ya yi awon-gaba da wata mota ƙirar Toyota Hilux.
Rahotanni sun bayyana cewa, ɓarawon ya samu shiga gidan ne ta ƙofa ta 4 inda ya fice da motar da misalin ƙarfe 5 na asubahin.
Majiyoyi sun ce, kyamarorin CCTV sun nuna cewa ɓarawon ya fita da motar ne ta babbar ƙofar gidan.
Haka kuma sun ce motar tana ɗaya daga cikin motocin tawagar mataimakin gwamnan jihar.
Wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa ana sanya ido ne a yankin ofishin mataimakin gwamnan a lokacin sa’o’in aiki ko kuma idan yana ofis.
A cewar majiyar, an ƙaddamar da bincike akan direban motar mai suna Shafi’u Sharp-Sharp, inda kuma aka tsare shi.
Saidai, ba a samu ji ta bakin Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Dawakin Tofa ba a lokacin kammala rahoton.
