Gwamnatin Zamfara ta yi alwashin tallafa wa sabuwar Jami’ar Kimiyya ta Tsafe

Spread the love

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi alƙawarin tallafa wa sabuwar Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Likitanci da Fasahar Lafiya da ke Tsafe jihar.

Hakan na ƙunse a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Dauda Lawal kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris, ya fitar a yau Talata a Gusau.

Idris ya ce, Gwamna Lawal ne ya bayyana wannan alkawari lokacin da ya karɓi shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Yakasai, tare da tawagar sa a ranar Litinin.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a fannoni biyu — ilimi da lafiya domin nuna cikakken ƙudirinta na farfado da waɗannan ɓangarori a jihar.

“Ku tabbata cewa gwamnati na za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga jami’ar. Za mu kuma ci gaba da neman ƙarin tallafi,” inji Gwamna Lawal.

A nasa bangaren, Farfesa Yakasai ya yaba wa gwamnan bisa kokarinsa na farfaɗo da harkokin ilimi da lafiya a jihar.

By Babaji