‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 20 bisa zargin fyaɗe

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Waɗannan da aka kama na daga cikin mutane 120 da rundunar ‘yan sandan suka kama kan laifuka daban daban.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a hira da manema labarai a ofishin sa.

Ya ce haka kuma a cikin waɗanda da aka kama mutane 18 ana zargin su da fashi da makami sai wasu 28 da ake zargi da laifin kisan kai, da mutum 28 da suma ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa waɗannan da aka kama ya zuwa yanzu an gabatar da 97 a gaban kotu sai mutum 22 da har yanzu ‘yan sanda na bincike a kan su da zaran an kammala binciken za a gabatar da su a gaban kotu.

Ya ce ‘yan sandan sun sami nasarar ƙungiyar da mutane 47 da yan bindiga suka garkuwa da su a sassan jihar da mutum 39 da akai kokarin Safar su zuwa kasashen waje dukkan sun kubuta kuma tuni yan sanda suka sada su da Iyalan su.

DSP Sadiq ya ƙara da cewa a lokacin da ‘yan sandan samamen kama waɗannan waɗanda ake zargin,sun gano bindiga biyu,kirar AK47 da kuma ɗayan ƙirar gida.

“Yan sanda sun kuma gano motoci guda uku da baburan hawa huɗu da kuma keken hawa mai ƙafa uku guda ɗaya,”inji Sadiq.

Sun kuma kama dabbobi guda 101 da suka haɗa da Shanu guda 76 da Awaki guda 27 sauran akwai miyagun ƙwayoyi, allurar Fentanyi injection mai sa maye, tabar wiwi ma dinbin yawa da wayar wutan lantarki na turakun manyan hanyoyi.

By ukarofi