Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata sanarwa da ta fito daga jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi a jihar Malam Danjuma Sani,ya ce duka makarantun firamare da na Sakandare a faɗin jihar aka basu umarni da su rufe saboda yanayin tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati nan na bibiyan yanayin tsaro a Arewacin kasan kafin ɗaukar mataki.
Wannan mataki da gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauka na zuwa ne bayan da ‘yan bindiga suka sace ‘yan mata 25 a wata makaranta a jihar Kebbi.
Haka kuma bayan afkuwar haka, aka sake samun labarin sace wasu ɗalibai mata a jihar Neja.
Yanzu dai al’ummar da ke zaune a jihohin Arewacin ƙasar nan na zama cikin zullumi da fargaba na irin abinda ka iya afkuwa dangane da hare haren ‘yan bindiga musamman a makarantun firamare da sakandare a yankin.
