
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya nuna damuwa kan janyewar jami’an tsaro mintuna kaɗan kafin ƴan bindiga su kai hari su sace ‘yan mata 25 a makarantar Maga ta Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu da ke jihar.
Ya bayyana cewa gwamnati ta samu bayanan leƙen asiri daga hukumar tsaro ta DSS, lamarin da ya sa aka tura ƙarin jami’an tsaro zuwa makarantar.
Gwamnan ya ce, sojoji sun janye da misalin 3:00am, sannan ’yan bindiga suka kai hari 45 mintuna bayan haka.
Ya kuma yi kira ga rundunar sojoji da ta yi binciki akan musabbabin janye jami’an tare da ɗaukar matakan da suka dace akan waɗanda ke da alhalin hakan.
A wani labarin kuma, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) Joe Ajaero, ya ce sace ’yan matan babban al’amari ne na ƙasa, inda kuma ya yi kira da a yi addu’a tare da guje wa siyasantar da batun tsaro.
Ajaero ya nemi hukumomin tsaro da su fifita aminci ɗaliban tare da ceto su a duk inda suke.
