Yanzu-yanzu: Mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa ƴan mata 13 a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da wasu ƴan mata guda 13 a yankunan manoma da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a Gundumar Mussa yayin da ƴan matan suke tsaka da aiki a gonaki, inda kwatsam sai mayaƙan zagaye su tare da yin awon-gaba da su.

Maitaimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Hon. Abdullahi Askira ya tabbatar da aukuwar lamarin a yau Lahadi.

Askira, wanda shi ke wakiltar mazaɓar Askira-Uba ya ce ƴan matan ƴan shekaru 15 ne zuwa 20, waɗanda suak je gona domin nome abin da aka shuka.

A cewarsa, ƴan matan suna daga cikin waɗanda gwamnati ta sauya wa sheƙa daga yankin Huyim zuwa Mussa, wanda yanki ne na noma kan matsalolin rashin tsaro.

Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikinsa ta yi nasarar tsira daga komar mayaƙan tun da safiyar Lahadi.

Da yake jawabi game da al’amarin, Sanatan yankin Borno ta Kudu Mohammed Ali Ndume, ya yi alla-wadai da harin inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da yunƙura wajen ganin an ceto sauran ba tare da wata illa ta same su ba.

By Babaji