
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin ɗaliban St Mary’s Catholic School, Papiri a Jihar Neja su guda 50 da aka yi garkuwa da su ne suka yi nasarar kuɓuta daga hannun ƴan bindiga tare koma wa cikin iyalansu.
Hakan na nufin har yanzu akwai sauran ɗaliba 253 da malamai 12 da ke hannun waɗanda suak yi garkuwa da su.
Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) a jihar kuma shugaban makarantar, Reberen Bulus Dauwa Yohanna ya sanar da haka ga manema labarai a yau Lahadi.
Wannan shi ne nasara na farko da aka sami akan al’amarin tun bayan faruwarsa a rare Juma’a.
Ya ce, ɗaliban sun yi tsere ne a tsakanin ranar da aka sace su da ranar Asabar, lamarin da aka tabbatar a lokacin da aka riƙa kiran iyalansu domin jajenta musu.
Ya kiam yi kira da a kwantar da hankula tare da cigaba da yin addu’o’i a yayin da jami’an tsaro ke cigaba da ƙoƙarin ganin an ceto sauran waɗanda iftila’in ya afka wa.
