A shirye nake na gabatar da hujjata – Natasha kan ƙarar biliyan N200 da Akpabio ya shigar akanta

Spread the love

Sanatar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ta shirya tsaf domin gabatar da shaidu a kotu bayan da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya shigar da ita ƙarar biyan sa Naira biliyan 200 akan zargin ɓata masa suna.

Akpabio na tuhumar Natasha ne bisa zargin ta masa laifin cin zarafi a bainar jama’a, lamarin da ta ce yanzu kotu za ta ba ta damar da majalisa ta ƙi bayarwa wajen sauraron ƙorafinta.

An tsayar da ranar farko ta sauraron shari’ar a 21 Janairu 2026, kuma ana sa ran dukkan ɓangarorin biyu za su gabatar da hujjoji.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a, Sanata Natasha ta bayyana cewa ta samu takardar shari’ar da Akpabio ya shigar mai darajar biliyan N200, lamarin da ta ce zai ba ta damar bayyana gaskiyar abin da ya faru.

Natasha ta nuna cewa duk da cewa ba za ta iya kai ƙarar kanta kai tsaye kotu ba a wancan lokacin bisa dokar Majalisar Dattawa da ke buƙatar a fara gabatar da irin wannan matsala a gaban kwamitin, yanzu ta ce wannan sabon ƙarar ya buɗe mata hanya ta bayyana gaskiyar abubuwan da suka faru.

Kazalika, ta ce daga lokacin da ta nuna rashin amincewa da abin da ta bayyana a matsayin buƙatun cin zarafi daga Akpabio, sai aka soma kai mata hare-hare marasa dalili da kuma matsin lamba a harkokinta na siyasa da rayuwa.

By Babaji