
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Lahadi wata tawagar dakarun sojin ƙasar Jamhuriyar Benin ta sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon, wanda aka tsara zai sauka a karagar mulkin a watan Afrilu mai zuwa bayan shekaru 10 a kujerar.
Sojojin, waɗanda ke kiran kansu da “Military Committee for Refoundation” (CMR), a wata kafar talabijin, sun ce sun tattauna a tsakaninsu inda suka cimma matsayar tsige shugaban ƙasar.
A yanzu haka dai ba a san inda Shugaba Talon yake ba, sannan ofishin jakadancin Faransa kamar yadda ya wallafa ta kafar X, ya ce an jiyo harbe-harben bindiga a yankin gidan shugaban ƙasar da ke Camp Guezo. Ya yi kira ga ƴan Faransa da su kasance a gidajensu saboda barazanar tsaro.
To saidai kuma, Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma sojoji suna cigaba da karɓe iko da gwamnatin ƙasar.
“Wannan ƙaramar tawaga ce ta mutanen da ke juya talabijin”, inji ofishinsa.
