Hukumar gidan gyaran hali ta ziyarci Sarkin Kabin Argungu

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukumar gidan gyaran hali reshen ƙaramar hukumar Argungu ƙarƙashin jagorancin babban Sufurtanda Lauwal Yeldu ta ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera.

Da ya ke jawabi yayin ziyarar Yeldu ya bayyana irin nasarorin da gidan da ke reshen ƙaramar hukumar Argungu ya samu a ƙarƙashin jagorancinsa sun haɗa da kimanin mutane ashirin suka sauke Al’ƙur’ani Maigirma, aƙalla sama da mutane arba’in sun koyi sana’o’in hannu daban-daban tare da samun ƙwarewa a cikin sana’o’in da suka haɗa da ƙere-ƙere da saƙe-saƙe wanda yanzu haka wadansu daga cikin su sun cigaba da sana’o’in bayan sun kammala wa’adin su na zaman gidan. Yanzu haka sun zama mutanen kirki sun dogara ga kawunan su har ma suna taimakon waɗansu a cikin al’umma.

 Ya kuma yaba wa Basaraken bisa ga irin kulawar da ya ke baiwa wannan gidan ta hanyar taimakawa da kayan abinci da na buƙatun yau da kullum.

Da ya ke mayar da jawabi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya bayyana farin cikin sa bisa ga wannan ziyarar tare da alwashin cigaba da tallafawa hukumar gidan a duk lokacin da bukatar haka ta taso.

Ya kuma shawarci jami’an da su ji tsoron Allah wajen aiwatar da ayukan su musamman a wajen mu’amalar su da mutanen da ke ƙarƙashin kulawarsu.

By ukarofi