A wata hira da ya yi da kafar IMI Media Group da ke ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Jakadan Amurka a Turkiyya kuma Jakadan Musamman kan batun Siriya, Tom Barak, ya yi wani bayani mai girgiza duniya, inda ya ce Amurka ta yi ƙoƙarin kifar da gwamnatin Iran sau biyu, amma babu ɗaya da ya yi nasara.
Hirar, wadda aka wallafa a shafin jaridar The National a ranar Juma’a, ta haɗa da bayanan da Barak ya yi game da manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. A cewarsa:
“Mun yi yunkurin sauya gwamnati a Iran sau biyu, amma dukkaninsu sun kasa yin tasiri.”
Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Amurka, Donald Trump, ba ta goyon bayan kawo sauyin gwamnati a Iran ta hanyar tilas. Ya ce tarihi ya nuna irin wannan dabarar ba ta taɓa haifar da ɗa mai ido ba.
A cewar Barak, tun daga shekarar 1946 zuwa yau:
“Amurka ta shiga harkokin juyin mulki da sauyin gwamnati har 93, amma duk sun gaza cimma burin da aka sa gaba.”
Ya ƙara da cewa manyan jami’an gwamnati irin su Marco Rubio (Sakataren Harkokin Waje a lokacin) da Shugaba Donald Trump, ba su da niyyar sake tsunduma irin waɗannan dabaru. Maimakon haka, “Suna neman matsayar da yankin kansa zai jagoranta. Wannan lamari na shafar Isra’ila ne fiye da Amurka.”
Lamarin ya ƙara tada jijiyoyin wuya a tsakaninsu da Iran, musamman a wannan lokaci da ake fama da tashin hankali a yankin.
