Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya musanta zargin iƙirarin da Bello Turji ya yi cewa manufofin gwamnatinsa ne suka rura wutar ayyukan ‘yan bindiga a Sakkwato da Zamfara.
Bafarawa ya ce ayyukan ‘yan bindiga bai zama ruwan dare a lokacin da ya sauka daga gwamnan Sakkwato ba a jiharsa ko a Zamfara a 2007 ba.
Kuma ya ƙara da cewa bai san dalilin da ya sa Turji ya alaƙanta shi da abubuwan da ke faruwa bayan shekaru da sauka daga mulki ba.
Turji, a wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Lahadi, ya zargi Bafarawa da tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Yerima, da fara assasa ƙwace burtalan kiwo da kafa ƙungiyoyin bijilanti waɗanda ya yi zargin suna kashe Fulani.
Wannan abu ya samo asali ne a lokacin da Musa Kamarawa, ɗan uwan Bafarawa, wanda ya taɓa zama mai taimaka wa tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi shi da rura wutar ayyukan ta’addanci.
Kamarawa ya yi zargin cewa Matawalle na da alaƙa da wasu ‘yan ta’adda kuma yana shagwaɓa su.
Kamarawa ya yi iƙirarin cewa Matawalle ya bai wa Turji da wasu ‘yan bindiga a Zamfara kyautar gida da motoci ƙirar Hiluɗ.
Sai dai Turji ya musanta iƙirarin Kamarawa a faifan bidiyon yana cewa akwai wasu ‘yan siyasa da suke amfani da Kamarawa domin ya yi masa karya a yayin da suke ƙoƙarin ɓoye laifukan da ɗan uwansa Bafarawa ke yi.
“Idan akwai wanda za a zarga da ta’addanci, shi ne mahaifinka, tsohon gwamnan Sakkwato da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmad Yerima, saboda su ne suka sace tare da sayar da burtalan kiwo da kafa kungiyoyin bijilanti waɗanda ke kashe Fulani.
“A garinka na karamar hukumar Isa a Sakkwato, kilomita ɗaya daga gidanka akwai burtalin kiwo.
Mahaifinka ne ya sayar. Akwai kusan burtalai 5 a gabashin garin Isa waɗanda dukkansu mahaifinka (Mr Bafarawa) ne ya karkatar da su. Waɗannan su ne mutanen da suka assasa tare da rura wutar rikicin,” inji Turji.
Kamarawa dai ya fito ne daga ƙaramar hukumar Isa da ake jihar Sakkwato inda ayyukan ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.
Martanin Bafarawa:
Sai dai Bafarawa, wanda ya zama gwamnan Sakkwato tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa bai taɓa goyon bayan kowanne irin abu da zai haifar da hatsaniya ba.
Gwamnan ya ce, duk yadda aka yi Turji yana mafarki ne ya ambaci sunansa cikin waɗanda suke ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya inda yake mai sa shi shiga irin wannan aiki abu bayan sauka daga mulki shekaru 20 da suka wuce.
“Bello Turji yana ina ne a lokacin da nake gwamnan Sakkwato kuma shekarunsa nawa? Ba abin da ya haɗu da shi.”
“Me zan amfani da ta’addanci a shekaruna,?”
“Abu ne za ya girgiza da jin mutum kamar ni yake yi wa karya . Wasu ne suke amfani da shi domin yi mana ƙarya.”
“Ina cigaba da ƙoƙarin ganin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ƙasata.”
