
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman gaggawa na Majalisar Zartarwa (FEC) a Fadar Shugaban Ƙasa yayin da yake gab da gabatar da Kasafin Kuɗin shekerar 2026 ga Majalisar Dokoki.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da zaman ne sa’o’i kaɗan da shugaban ƙasar ya sanar da majalisa ƙudirinsa na gabatar da kasafin a yau Juma’a da misalin ƙarfe 2 na rana kamar yadda dokar ƙasa ta bada dama.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce an shirya zaman ne domin bada damar gabatarwa ta ƙarshe bayan kammala aikin tantance kasafin gabanin bayyanawa a gaban ƴaƴan Majalisar Dokokin.
A cewar Shettima, zaman gaggawar yana da muhimmanci musamman wajen nazari akan ƙididdige saɗaororin kasafin, tabbatar da hasashen kasafin, kashe-kashe da sauransu.
Hakan na zuwa ne bayan wani zaman irinsa da aka yi a ranar 3 ga watan Disamba inda aka duba tare da tabbatar da muhimman al’amuran kashe-kashen tsakiyar zango (MTEF) da takardar dabarun kasafi (FSP) waɗanda sune ginshiƙan kasafin.
