Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Akwai misalai da dama wadanda wasu malamai kan yi kuskuren bada fatawa. Amma babban dalilin yin irin wadannan kura-kurai sune: Na farko watsi da akan yi wajen daukar koyarwar ƙur’ani farko a kan duk wani irin hukunci. Sannan na biyu, watsi da ainihin duba yadda Annabi ya rayu a kan mas’alar da a ke kokarin bada fatawar a kai. Na uku shine fifita Fiƙihu akan wadancan guda biyun, da kuma wasu lokatai fifita al’adar larabci a kan ta musulunci. Sannan a karshe watsi da yin tunani a kan matsala domin yarda kawai da cewa wasu Salaf sun tafi a kan wata mahanga.
Idan muka dauki wannan fatawar ta Jalo Jalingo, wadda malamai da dama sun tafi a kanta, muka dora ta a sikelin wadancan abubuwa da na jero, za mu fahimci karfin bayanin da na ke yi.
1. Allah ya umarce mu a ƙurani cikin Suratul Maida cewa: Q4:34 “Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu.”
Tsayuwa, wato kulawa da kariya, hakkin namiji ne a kan matarsa. Don haka akwai abinda ya fi kulawa da lafiyarta cikin wannan hakki? Shin lafiya ba ta ma fi ciyarwa ba? Iyayenta ke ciyar da ita? Babu sanda mace ke bukatar kulawar mijinta fiye da idan ta na lalura, amma al’ada da gurguwar fatawa na sa maza gujewa wannan nauyi su dorawa iyaye. Za a iya samun yanayi da zai sa iyaye su shigo cikin jiyyar yar su, amma hakkin jiyya na miji ne kamar yadda Allah ya umarta a wannan aya.
2. A hadisin Bukhari 3698 wanda Tirmidhi ma ya ruwaito irinsa, Annabi (SAW) ya umarci Usman Bn Affan ya zauna a Madina kada ya bi su wajen yakin Badar, sakamakon matarsa, Ruƙayya, wadda ‘ya ce ga rasulillah, ba ta da lafiya. Saboda haka duk da cewa babu abinda ya kai girman Jihadi, amma Annabi ya umarci Usman ya zauna jiyyar matarsa fiye da fita yaki. Bai kuma ce a dauko masa ‘yar sa a dawo da ita gidansa ba ko?
3. Fifita al’adar larabci, ko ta wata al’umma na kasancewa a karbi wata koyarwa fiye da ta addini. A kasar Hausa kafin zuwan musulunci har zuwa yau, akasari idan ciwon mata ya yi tsanani, ko ta haihu, za ka samu ana kaita gidan iyayenta jinya ko wanka. Wannan al’ada ce ta bahaushe amma an kurdo ta da karfin tsiya sai ta shiga tsarin addini, kamar yadda su Jalo Jalingo ke kokarin cusawa.
4. Fiƙihu: Akasarin fatawoyi da aka gina daga Fiƙihu, za ka samu cewa fahimta ce ta wasu malamai wadda ta ke daidai da zamaninsu da fahimtar su da ayoyi ko hadisai. Kamar yadda su ke da wannan yancin, haka Malaman kowane zamani ke da wannan yancin na nazari da bincike (ijtihadi) don samar da mafita ta matsalolinsu. Amma sai ake dagewa cewa dole ne a bi malaman baya (Salaf) Ido rufe, babu ja da duk wata fahimta ta su. Akwai kuskure a cikin haka, wanda ke sanya a yi ta zama cikin kuskuren. Misali Imam Nawawi ya na da fatawar cewa mace ba ta da hakkin yiwa miji girki, duk da cewa shi Al Nawawi bai ma taba aure ba, sannan kowa ya ga matan Annabi sun yi masa girki. Shi ya sa yanzu zaka sami mata yan Boko na cewa su girki bai wajaba a kansu ba (duk da tsawon rayuwarta uwarta ke girka musu abinci) ko a wannan fatawa cewa jiyyar mata bata wajaba a kan miji ba.
5. A karshe, matukar malamai ba za su rika tunani ba, tabbas za a yi ta samun fatawoyin da za su rika karo da ƙurani, hadisi da hankali. Shi ya sa dole daliban Ilimi su fadada zukatansu su rika nazari da bincike. Allah ya datar da mu gaba daya.
Malam Ali Abubakar manazarci ne a Kano
