Daga HABU ƊAN SARKI, a Jos
Gwamnan Jihar Filato Caleb Manasseh Mutfwang ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC a hukumance, bayan raɗe-raɗin da aka riƙa yi a baya.
Cikin rakiyar da ɗaruruwan magoya bayansa da wasu muƙarrabansa daga cikin gwamnati, Gwamnan ya sanar da komawarsa Jam’iyyar APC ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Jos.
Gwamnan wanda tun da farko ya sanar da fitarsa daga Jam’iyyar PDP awa ashirin da huɗu kafin ya koma jam’iyyar APC, ya ce ya yi haka ne domin kawo wa jihar Filato cigaba.
A wata sanarwa da kakakin fadar Gwamnatin Jihar Filato, Gyang Bere ya fitar an bayyana cewa, Gwamna Caleb Mutfwang yana da ƙwarin gwiwar wannan mataki da ya ɗauka shi ne ya fi dacewa da halin da jihar take ciki a yanzu. Ya yi wa Jam’iyyar PDP godiya da damar da ta bashi na zama Gwamna,da goyon bayan da take bashi a tafiyar siyasar sa.
Ya sake jaddada aniyarsa ta cigaba da tafiya da kowanne ɓangare na jihar, ba tare da nuna wariya ko bambanci ba. Yayin da ya ƙara da cewa, zai yi amfani da wannan dama wajen ganin Gwamnatin Tarayya ta kawo wa Jihar Filato ayyukan cigaba da jama’a da dama za su amfana.
A wata sanarwa da ya fitar tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Jonah David Jang ya yi kira ga magoya bayan Jam’iyyar PDP da suka rage, da su kwantar da hankalin su kuma su cigaba nuna goyon baya da kishin da suke da shi, wajen kare manufofi da muradun jam’iyyar. Kada wannan canjin sheƙa da Gwamnan Jihar ya yi ya girgiza su.
Jang, ya yi wa Gwamna Mutfwang fatan alheri da fatan zai cigaba da ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansa kamar yadda ya ɗauki rantsuwar haka. Haka su ma sauran abokan tafiyarsa da za su bi shi APC, Sanata Jang ya nemi da duk inda suka shiga kada su manta su ýan Jihar Filato ne.
