
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron rantsar da Shugaba Mamadi Doumbouya na ƙasar Guinea-Conakry.
Haka kuma, Shettima zai halarci taron shekara-shekara karo na 56 na Harkokin Tattali na Duniya a Birnin Davos na Switzerland bayan rantsa da shugaban ƙasar Yammacin Afirkan.
Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha a wata takarda da ya aike wa manema labarai, ya sanar da haka.
Ya ce, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai wakilci Shugaba Tinubu a taron rantsarwar Shugaba Doumbouya a ranar Asabar, a Filin wasa na GLC da ke Nongo a Conakry.
Samun wakilcin Nijeriya a taron dabara ce da ƙarfafa alaƙar shugabanci tattali da haɓakar harkokin tattali a matakin duniya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata na Tinubu.
Ya bayyana cewa, baya ga haka ziyarar ta kuma ƙunshi ƙarfafa alaƙar kasuwancin da ke tsakanin ƙasashen biyu musamman wajen kai kayayyakin da aka samar da na amfani gona daga Nijeriya zuwa ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa Dala miliyan 3.29.
Daga Guinea, Shettima zai tafi Switzerland domin halartar taron tattalin, wanda za a fara daga ranar 19 zuwa 23 ga Junairu, 2026.

