
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ce gwamnatinsa tana gina titina guda 140 a baki ɗaya ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar, waɗanda jimillar tsawonsu ya kai kilomita 1,335.
Ya bayyana cewa, gwamnatin a halin yanzu ta fara aikin kowannensu, yana mai ƙarawa da alƙawarin kammala ayyukan da ya gada daga gwamnatocin baya.
Uba Sani ya faɗi haka ne a jiya Asabar, a lokacin da yake ƙaddamar da titin asphalt da ya haɗa Durum zuwa Kuruntumawa a Ƙaramar Hukumar Maƙarfi, inda ya ce dukkan ayyukan titinan ana gudanar da su bisa inganci.
Ya ce, a watan Satumbar 2025 ne ya je Kuruntumawa domin buɗe aikin titin, wanda aka yi bikin fara amfani da shi a jiya.
Fara amfani da wannan titi zai taimaka wajen sauƙaƙe wa manoma da ƙananan ‘yan kasuwa safarar kayayyakinsu, waɗanda a baya suke fuskantar matsi a sakamakon rashin kyan hanya. Haka ma ga zirga-zirgar ɗalibai da masu zuwa asibiti da ke fuskantar jinkiri yayin tafiyar da harkokinsu.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyarsa ta cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na raya karkara da damawa da talakawa a birane da ƙauyuka.
Kazalika, ya ƙara da cewa Maƙarfi ɗaya ce daga cikin ƙananan hukumomi 12 da ba su taɓa samun aikin titi ba a tsawon shekaru 12.
