
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shigarsa jam’iyyar APC a hukumance, kwanaki kaɗan da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
An gudanar da taron sauya sheƙar ne a Gidan gwamnatin Kano, tare da rakiyar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar.
A yayin jawabin da ya gabatar a wurin taron, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa daga yanzu ya daina makauniyar biyayya a musamman a harkar siyasa.
Ya ce, zai cigaba da fifita muradun jihar da al’ummarta wajen inganta dukkan al’amuran da za su taimaka wajen ciyar da su gaba.
Gwamnan ya ƙara da cewa matakin da ya dauka ya samo asali ne daga ƙoƙarinsa na neman kare martabar al’umma, ci-gaban jihar, da kuma tabbatar da walwalar jama’arsa ba tare da la’akari da matsin lamba daga kowace fuska ba.
Shigarsa jam’iyyar APC ta haifar da cece-kuce a fagen siyasar jihar Kano da ma arewacin Nijeriya duba da yadda hakan ya nuna an samu sauyi mai girma a tsarin siyasar Kano.
