
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga ƙasar Libiya sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun halaka Saif al-Islam Gaddafi, wanda ɗan tsohon shugaban ƙasar Marigayi Muammar Gaddafi ne.
A cewar Al Jazeera ana ganin an harbe Saif al-Islam ne a yankin Zintan da ke Yammacin Libiya inda a nan yake zaune tsawon shekaru da dama.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin kashe Saif al-Islam ba.
Wata ‘yar uwarsa ta shaida wa gidan talabijin na ƙasar cewa ya mutu ne a kusa da iyaƙar ƙasar da Aljeriya, ba tare da bayyana ta yadda ya mutu ba.
An daɗe ana daukarsa a matsayin wanda zai gaji mahaifin nasa Kanal Gaddafi.
Bayan hamɓarar da gwamnatin mahaifinsa a shekara ta 2011, an kama tare da tsare shi a birnin Zintan na tsawon shekara shida.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta nemi a kama shi kan laifukan take haƙƙin ɗan’adam a lokacin da aka murƙushe masu zanga-zanga a 2011.
Mai taimaka masa akan harkokin siyasa, Abdallah Othman ne ya sanar da rasuwar Saif mai shekaru 53.
