Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar sun ceci aƙalla jihohi 27 na Nijeriya daga faɗawa halin durƙushewar tattalin arziki.
Idris ya yi wannan bayani ne yayin da yake gabatar da lakca a bikin yaye ɗalibai karo na 34 da kuma bikin cika shekaru 43 da kafuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, a ranar Asabar.
Lakcar da ministan ya gabatar ta mayar da hankali kan rawar da matasa za su taka wajen gina ƙasa a wannan zamani na sauye-sauyen manufofin gwamnati, inda ya jaddada cewa gyare-gyare su ne tubalin ci gaban kowace ƙasa.
A cewarsa, kafin ranar 29 ga Mayun 2023, jihohi da dama a Nijeriya na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi har ta kai ga gaza biyan albashin ma’aikata.
Ya ce: “Shugaba Bola Tinubu ya zagaya sassan Nijeriya tun lokacin yaƙin neman zaɓe, yana bayyana manufofinsa na ganin ƙasar nan ta zama mafi ƙarfi. Bayan hawansa mulki, ya fara aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da suka ceci yawancin jihohi daga faɗawa halin durƙushewa.”
Ministan ya ƙara da cewa, a yanzu jihohi na karɓar kuɗaɗen shiga fiye da sau uku na abin da suke samu a baya, lamarin da ya ba su damar biyan albashi, aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da kuma isar da roman dimokiraɗiyya ga al’umma.
Idris ya jaddada cewa sauye-sauyen sun kasance masu wahala a matakin farko, amma sun zama dole domin gyara kura-kuran da aka gada da kuma shimfiɗa tubalin ingantaccen ci gaba na dogon lokaci.
Ya ce babu wata ƙasa da za ta samu ci gaba mai ɗorewa ba tare da aiwatar da gyare-gyare ba, yana mai cewa dakatar da gyara na iya jefa ƙasa cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.
Ministan ya kuma yi kira ga matasa da su fahimci cewa wannan zamani na sauyi na buɗe sababbin damar tattalin arziki, fasaha da ƙirƙira, inda ya ce su ne za su amfana matuƙa idan suka yi amfani da damar da ke tattare da sabbin tsare-tsaren gwamnati.
A ƙarshe, ya bayyana cewa shugabanci mai hangen nesa da jajircewa wajen aiwatar da gyare-gyare ne zai tabbatar da ɗorewar cigaban Nijeriya da ƙarfafa tubalin gina ƙasa.
