NNPP ta musanta kalaman Kwankwaso na jagoranci a gaban alƙalan Kotun Ƙoli a shari’ar zaɓen 2019

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar NNPP ta yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa daga cikinta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso inkari, bisa kalamansa na cewa ya je da Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen wasu alƙalan Kotun Ƙoli a 2019.

NNPP ta tirje akan lallai Kwankwaso ba ɗan jam’iyyar ba ne a 2019 lokacin da al’amarin shigo da alƙalan ya faru, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa ya bayyana haka a ƙarshen mako inda ya nesanta kansa da zargin wanda aka jingina wa Kwankwaso, sannan ya nemi Ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa (NBA) da ta gaggauta cire sunan NNPP daga dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar wa Sufeto Janar na ‘yan sanda akan batun.

A sanarwar da Sakatarenta na ƙasa, Kwamared Oginni Olaposi Sunday ya fitar, jam’iyyar ta bayyana rahotannin da ke alaƙanta ta da saɓanin a matsayin “abin ruɗarwa kuma ba daidai”.

“Mu a nan muna da tarihin komai a rubuce. Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba mamban NNPP ba ne a 2019 a lokacin da aka yi zargin ya ɗauki Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa ganawa da alƙalan Kotun Ƙoli” inji Oginni.

A cewar sanarwar, Kwankwaso ya shiga NNPP ne ‘yan watanni kafin babban zaɓen 2023 tare da wasu sanannun ‘yan siyasa kamar su Buba Galadima, Farfesa Alƙali, Sanata Suleiman Hunƙuyi, Farfesa Hanga da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Haka kuma jam’iyyar ta ƙaryata ikirarin da ke cewa Kwankwaso na daga cikin waɗanda suka samar da NNPP, inda ta ce Dakta Boniface Okechukwu Aniebonam ne sahihin wanda ya kafa jam’iyyar.

Kazalika, NNPP ta zargi tsohon ministan tsaron da yunƙurin ƙwace jam’iyyar bayan shigarsa cikinta, inda ta kuma zarge shi da sauya bajinta da mayar da kalolinsa na tafiyar Kwankwasiyya ba tare da amincewar wanda ya kafa ta ko kwamitin amintattunta ba.

Har ila yau, NNPP ta jaddada aniyarta ta korar Kwankwaso daga jam’iyyar, matakin da ta ɗauka tun da jimawa.

A ƙarshe, ta ce sahihan jagororinta sune Dakta Boniface Okechukwu Aniebonam a matsayin wanda ya samar kuma shugaba, sai kwamitin amintattu da ya haɗa da Dakta Agbo Gilbert Major a matsayin shugaban na ƙasa; da kuma Kwamared Oginni Olaposi Sunday a matsayin Sakatare na ƙasa.

By Babaji