Bayan shekara 37 Tinubu zai yi ziyarar aiki a Birtaniya a matsayin shugaba daga Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

hugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Ƙasar Birtaniya daga ranar 18 zuwa 19 ga Maris, 2026 sakamakon gayyatarsa a hukumance daga Sarki Charles na Uku.

Sanarwar ziyarar ta fito ne a ranar Lahadi ta shafin X na Masarautar Birtaniya, inda aka bayyana cewa Sarki Charles III da Sarauniya Camilla za su karɓi Shugaba Tinubu a fadar Windsor Castle.

Shugaban zai kasance tare da matarsa kuma Uwargidan Shugaban Ƙasa, wato Sanata Oluremi Tinubu.

A nasa ɓangaren Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, inda ya ce ita ce ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai Birtaniya acikin shekaru 37, yana mai jaddada cewa Tinubu zai kasance tare da Uwargidan nasa yayin ziyarar.

Ziyarar ƙarshe da wani shugaban Nijeriya ya kai Birtaniya an yi ta ne a shekarar 1989, lokacin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda Marigayiya Sarauniya Elizabeth ta II ta karɓe shi na tsawon kwanaki huɗu.

Shugaba Tinubu da Sarki Charles III, waɗanda duka suka hau mulki a watan Mayun 2023, sun haɗu sau da dama musamman a lamuran da suka shafi raya ƙasa da ci-gaban al’umma.

By Babaji