Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shekaru 30 bayan hatsarin jirgin sama da ya yi sanadin rasuwar Ibrahim Sani Abacha, babban ɗan tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja ta Nijeriya, wato Janar Sani Abacha, lamarin na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan al’amura masu cike da ruɗani a tarihin siyasar ƙasar.
A wani rahoto da jaridar Newspoint ta wallafa, ta ce, a yau da ake cika shekaru talatin da rasuwar tasa, tambayoyi da jita-jita game da haƙiƙanin abin da ya faru a ranar 1996 sun sake dawowa fili, lamarin da ya bar alamar baƙin ciki da rashin amsoshi a zukatan mutane da dama.
A ranar Alhamis, 18 ga Janairu, 1996, jaridun Nijeriya sun fito da kanun labarai iri ɗaya – mutuwar Ibrahim Abacha. Matashin mai shekaru 29 ya rasa ransa ne a wani hatsarin jirgin sama mallakin fadar shugaban ƙasa, wanda ya faɗi a kusa da birnin Kano. Dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun mutu a wurin. Rahotannin farko sun nuna gobarar injin jirgi a matsayin abin da ya haddasa hatsarin.
Hatsarin ta faru ne a lokacin da Nijeriya ke cikin tsananin yanayin siyasa a ƙarƙashin mulkin soja, abin da ya sa lamarin ya wuce na iyali kawai, ya koma babban lamari na ƙasa baki ɗaya. Jaridu a wancan lokaci sun bayyana hatsarin a matsayin mummunan al’amari da ya gigita al’umma.
Duk da cewa wasu jaridu sun bayyana ranar 18 ga Janairu a matsayin ranar hatsarin, wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Janairu. Sai dai babu saɓani kan sakamakon – babu wanda ya tsira daga hatsarin.
Majiyoyi sun bayyana cewa jirgin ya tashi daga Legas da misalin ƙarfe 6:15 na yamma, ɗauke da Ibrahim Abacha tare da abokai, mataimaka da jami’an tsaro. Tun da farko a ranar, jirgin ya sauka a Makurdi, kuma an ce ba a daɗe da dawo da shi gyara daga ƙasar Switzerland ba, abin da ya sa ake zaton yana cikin lafiya.
Ana zargin Ibrahim ya je Kano ne domin ganawa da mahaifinsa yayin ziyarar jaje ga Sarkin Kano, tare da kammala wata harka ta sayen kadarori. Daga cikin mutanen da ke cikin jirgin har da Bello Dangote, ɗan uwan Aliko Dangote, da wasu fitattun mutane da jami’an tsaro.
Yayin da jirgin ke daf da sauka a filin jirgin saman Kano da misalin ƙarfe 8 na dare, ɗaya daga cikin injinansa ya kama da wuta. Rahotanni sun ce matuƙin jirgin ya sanar da hasumiyar kula da zirga-zirgar jirage, amma al’amura sun faru cikin sauri fiye da yadda za a iya ceto lamarin.
Mazauna ƙauyen Dausayi, kimanin kilomita 20 daga filin jirgi, sun ce sun ga wuta a sararin sama kafin su ji ƙarar fashewa sau biyu. Lokacin da masu aikin ceto suka isa wurin, jirgin ya ƙone ƙurmus.
An ce gawawwaki shida ne kawai aka iya ganowa da farko, ciki har da matuƙin jirgin da aka tarar a kujerarsa. Sauran gawarwakin sun ƙone sosai har ba a iya gane su. An kuma gano makamai da harsasai a wurin, abin da wasu ke ganin ya ƙara tsananta gobarar.
Bayan hatsarin, an ce Janar Sani Abacha ne da kansa ya sanar da matarsa, Inna Maryam, labarin rasuwar ɗansu. Bayan wasu kwanaki, wata ƙungiya da ba a san ta ba a baya mai suna “United Front for Nigeria’s Liberation” ta ɗauki alhakin harin a wata sanarwa da ta aikewa kafafen watsa labarai na ƙasashen waje. Sai dai fitattun ’yan gwagwarmayar dimokuraɗiyya sun yi watsi da iƙirarin, suna cewa babu hujja.
Rahotanni sun kuma ambaci wani fashewa a filin jirgin Kano a wancan lokaci, da kuma wani a Kaduna, lamarin da ya ƙara dagula yanayin tsaro da kawo ruɗani.
Masu bincike sun duba yiwuwar matsalar injin jirgi, kuskuren matuƙi, ko kuma matsalar kayan aikin filin jirgi. Wasu sun yi zargin jirgin ya yi nauyi fiye da kima, yayin da wasu majiyoyi na soja suka karkata zuwa matsalar injin. Duk da yawan hasashe, babu wanda aka kama ko aka tabbatar da hannu a lamarin, kuma rahotannin kwamitocin bincike ba su taɓa kawar da shakku gaba ɗaya ba.
Waɗanda suka san Ibrahim Abacha sun bayyana shi a matsayin mutum mai fara’a, kyauta da aminci ga na kusa da shi. Ana danganta shi da taimaka wa matasa da dama a harkokin kasuwanci da ayyukan kuɗi.
Yayin da ake cika shekaru 30 da rasuwarsa, ’yar uwarsa Gumsu Abacha ta rubuta saƙon tunawa mai cike da jimami, tana addu’ar Allah ya jiƙansa.
Har yanzu, hatsarin jirgin da ya kashe Ibrahim Abacha na ci gaba da zama alamar asara, iko da kuma ruɗani a tarihin Nijeriya. Shin haɗari ne kawai? Matsalar injin ne? Ko kuma wani abu daban? Wataƙila amsar ba za ta taɓa fitowa fili ba, amma labarin na ci gaba da rayuwa a zukatan mutane.
