
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Litinin Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa na shugabancin hukumar a hukumance.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, Farfesan ya ce ya ɗauki matakin ne bisa wasu dalilai na raɗin kansa da kuma shawarwarin da ya samu daga wasu daga cikin iyalansa.
A cewarsa, bisa la’akari da sashe na 3(6) na dokokin NAHCON gyaran 2006, ya miƙa takardar yin murabus a hukumance ga Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR).
A ranar Litinin ɗin ne wasu bayanai suka nuna cewa shugaban ya ajiye aikinsa ne sanadiyyar wasu ƙorafe-ƙorafe da aka miƙa game da shi.
Wani daga cikin jami’an hukumar alhazan ya tabbatar wa manema labarai da batun ajiye aikin shugaban, saidai bai yi ƙarin haske akan dalilan da suka sabbaba haka ba.
Bayanai sun nuna cewa wakilin kwamitin shugabancin hukumar ne ya tura ƙorafe-ƙorafe zuwa fadar shugaban ƙasa game da shugaban, kamar yadda wani rahoto ta BBCHausa ta wallafa ya bayyana.
A cikin shekaru uku zuwa huɗu da suka gabata, an rika samun sauye-sauye a shugabancin NAHCON, inda kusan shugabanni uku suka riƙe muƙamin amma suka yi murabus kafin cikar wa’adinsu.
A shekarar 2024 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Sheikh Abdullahi a matsayin shugaban hukumar bayan sauke tsohon shugabanta na riƙo Jalal Arabi, wanda daga baya Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta tsare shi bisa zarginsa da hannu a almundahana.
