Majalisar Wakilai ta umarci Akanta-Janar da Odita-Janar su kawo rahotannin shekaru huɗu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Wakilai ya umarci Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da Ofishin Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da su tattara tare da gabatar da cikakken rahoton haɗaɗɗen asusun Gwamnatin Tarayya da kuma rahoton binciken kuɗi na shekarun 2023, 2024 da 2025 kafin watan Oktoban 2026.

Umarnin ya fito ne a yayin zaman sauraron bahasi na bincike da aka gudanar a zauren Majalisar ƙasa, inda ‘yan majalisa suka nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen gabatar da rahotannin kuɗin gwamnati da aka tantance, tare da duba ingancin tsarin sarrafa kuɗaɗen jama’a a Nijeriya.

Shugaban kwamitin, Bamidele Salam, ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira maimaituwar saɓa wa tanadin doka daga ofishin Akanta-Janar wajen gabatar da rahotannin da aka tantance a kan lokaci. Ya tunatar da jami’an cewa dokar kula da alhakin kuɗi ta ƙasa ta wajabta wa gwamnatin tarayya wallafa haɗaɗɗen rahoton kuɗi da aka tantance cikin watanni shida bayan ƙarshen kowace shekara ta kuɗi.

A cewarsa, jinkirin da ake samu na tauye da’a a harkokin kuɗi, rage martabar hukumomi da kuma girgiza amincewar masu zuba jari.

Ya ƙara da cewa, jinkirin rahotanni a ɓangaren gwamnati na rage ƙarfin Nijeriya wajen jawo jarin ƙasashen waje da kuma samun tallafin abokan hulɗa na bunƙasa ƙasa, waɗanda ke buƙatar sahihan bayanai na kuɗi masu sabuntawa.

Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan biyan naira biliyan 9.8 ga masu kula da tsarin GIFMIS a shekarar 2024, yana tambayar ko an samu kimar da ta dace da kuɗin da aka kashe.

’Yan majalisar sun ce duk da sabunta kwangiloli domin inganta tsarin, har yanzu ba a samu cikakkiyar daidaituwar asusu da rahotanni cikin lokaci ba.

Wakilin Akanta-Janar na Tarayya, Shuaibu Sikiru, ya danganta jinkirin da matsalolin aiki da na tsari. Ya ce rashin samun cikakkun bayanan asusun banki daga CBN ga ma’aikatu, hukumomi da sassa daban-daban na gwamnati na daga cikin manyan ƙalubale. Haka kuma, ya amince cewa akwai matsalolin fasaha a tsarin GIFMIS, yana mai bayyana cewa cikakken daidaita asusun gwamnati na ƙarshe ya gudana ne a shekarar 2022.

Game da tsarin Asusun Bai ɗaya na Gwamnati (TSA), ya ce shigar da Remita a matsayin ƙofar biyan kuɗi ya faru ba tare da isasshen daidaitawa da ofishin Akanta-Janar ba, lamarin da ya haifar da tangarɗa da rarrabuwa wajen sarrafa bayanan kuɗi a tsakanin ma’aikatu.

Shi ma Mai Binciken Kuɗi na Tarayya, Shaakaa Chira, ya jaddada cewa akwai giɓin tsarin doka, inda kundin tsarin mulki bai fayyace takamaiman wa’adin da Akanta-Janar zai gabatar da rahoton kuɗi ba, duk da cewa dokar kula da alhakin kuɗi ta tanadi lokacin wallafa rahotannin da aka tantance. Ya ce ana kammala shirye-shiryen mika rahotannin bincike na shekarun 2022 zuwa 2025 ga Majalisar ƙasa.

’Yan majalisar sun gargaɗi cewa rashin samun sabbin rahotannin kuɗi na hana majalisar cika rawar sa ido yadda ya kamata, tare da yiwuwar tattaunawar kasafin kuɗi ta gudana ba tare da cikakken haske kan halin kuɗin gwamnati ba. A ƙarshe, kwamitin ƙarƙashin jagorancin Salam ya umarci ofisoshin biyu da su kammala duk wani rahoto da ya rage kafin Oktoban 2026, tare da gargaɗin cewa duk wata gazawa za ta jawo hukunci daga ɓangaren majalisa.

Kwamitin ya sake jaddada aniyarsa na ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kula da dukiyar jama’a yadda ya dace, yana mai cewa gabatar da rahotannin kuɗi cikin lokaci na da muhimmanci wajen dawo da amincewar jama’a ga tsarin kuɗin gwamnati.

By ukarofi