NITDA ta horar da matan ’yan majalisa amfani da fasahar zamani a fannin jagoranci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Bunaasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA), tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Matan ‘Yan Majalisar Wakilai (HORSA), sun ƙaddamar da wani shiri na kwanaki biyu a Abuja domin ƙarfafa ƙwarewar jagoranci na fasahar zamani ga matan ‘yan majalisar.

Taron, mai taken “ƙarfafa Mata Akan Fasahar Zamani: Jagoranci, ƙwarewa, Sama da Damarmaki”, ya mayar da hankali kan ilimin fasahar zamani, wayar da kai kan tsaron yanar gizo, ƙarfafa tattalin arziki, kasuwanci da kuma juriya ta fuskar lafiyar kwakwalwa — musamman ganin nauyin rayuwar jama’a da ke tattare da muƙaman siyasa.

Da take jawabi a wajen buɗe taron, uwargidan Kakakin Majalisar Wakilai, Fatima Tajudeen Abbas, ta jaddada cewa tsayuwar zuciya da kwanciyar hankali na da matuƙar muhimmanci ga matan masu riƙe da muƙaman gwamnati, duk da cewa ana yawan yin watsi da rawar da suke takawa.

Ta ce, “Akwai nauyin tsammanin jama’a, jadawalin aiki mai cike da nauyi da kuma duba da idon jama’a. A matsayinmu na mata, muna zama abokan shawara da ginshiƙan ƙarfafawa, muna samar da kwanciyar hankali a bayan fage.”

Ta ƙara da cewa, fahimtar muhimmancin lafiyar kwakwalwa ba alamar rauni ba ce, illa alamar ƙarfi da sanin kai, domin aikin gwamnati na buƙatar juriya da sarrafa motsin zuciya yadda ya kamata.

Fatima Abbas ta yi nuni da yadda fasaha ke sauya mu’amalar jama’a, inda ta ce bayanai na yawo cikin sauri a kafafen dijital, wasu lokuta ba tare da cikakken bayani ba. Ta yi gargaɗi kan yaɗuwar labaran ƙarya da barazanar da ke fuskantar yara a yanar gizo, tana mai kira ga mahalarta taron da su zurfafa fahimta kan sawun dijital (digital footprint), kariyar sirri da halayen amfani da intanet cikin hikima.

Ta yaba da haɗa darussa kan kasuwanci da tattalin arziƙin dijital a cikin shirin, tana mai cewa ƙarfafa mata ta fuskar tattalin arziƙi na haifar da gagarumar alfanu ga iyalai da al’umma baki ɗaya.

A nasa jawabin, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, ya bayyana matan ’yan majalisa a matsayin muhimman ginshiƙai a tsarin mulkin Nijeriya. Ya ce hidimar ƙasa ba ta tsaya ga zaɓaɓɓun shugabanni kaɗai ba.

Ya yaba da jagorancin Fatima Abbas wajen samar da haɗin gwiwa da NITDA, yana mai cewa shirin ya zo a kan lokaci, musamman a wannan zamani da fasaha ta zama ginshiƙin tattalin arziƙi da shugabanci.

Gbajabiamila ya ƙara da cewa, shirin ya dace da ajandar sauyin dijital na Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ciki har da shirin 3MTT da ke bai wa ‘yan Nijeriya ƙwarewar fasaha mai amfani.

Ya ƙarfafa mahalarta taron da su yi amfani da damar wajen inganta rawar jagorancinsu da yaɗa ilimin dijital a cikin al’ummominsu.

Ana sa ran kammala horon a ranar Talata tare da ƙarin zama kan kariyar yanar gizo, ilimin kuɗi da faɗaɗa rawar mata a tattalin arzikin dijital na Nijeriya.

By ukarofi