
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro na JTF da ke aiki a ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya sun yi nasarar daƙile yunƙurin ƙaddamar da wasu munanan hare-hare da ‘yan ta’adda suka shirya a ƙananan hukumomin Konduga, Marte, Jakana da kuma Mainok da ke Jihar Borno.
Mayaƙan ‘yan ta’addar sun ƙaddamar da hare-haren da misalin ƙarfe 10:30 na daren Juma’a har zuwa ƙarfe 3:00 na asuba, inda suka gaza samun nasara sakamakon tsayin daka da dakarun tsaron suka yi, kamar yadda jami’in yaɗa labaran atisayen, Laftanal Kanal Sani Uba ya bayyana a wata takarda da ya fitar a yau Juma’a.
A cewarsa, dakarun sun samu ɗauki daga sashe na 1 da na 2, lamarin da ya sa suka lallasa mayaƙan da tilasta musu janyewa daga yunƙurin nasu.
A wasu yankunan ma bayan kora su sai da sojojin suka kuma farmake su yayin da suke ƙoƙarin tserewa, kamar yadda jami’in ya shaida a takardar.
A yayin haka ne aka halaka da dama daga cikin jagororin ‘yan ta’addar da kuma mutanensu masu tarin yawa, inda kuma a gefe guda dakarun suka cigaba da gudanar da ikon sansanoninsu.
Ya ƙara da cewa, a yanzu haka dakarun suna cigaba da gudanar da atisayen bincike a yankunan da aka yi ba-takashin, inda aka gano gawarwakin ‘yan ta’adda, bindigunsu da sauran kayan yaƙi.
Har ila yau, ya ce wasu daga cikin sojojin sun rasu a yayin arangamar ciki har da wani jajirtaccen soja da ke jagorantar wasu dakaru wajen mayar wa mayaƙan ‘yan ta’addar martani.
