Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Litinin ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa ƙasar nan ba za ta lamunci duk wani abu da zai yi barazana ga zaman lafiya da haɗin kan Najeriya ba.
Shugaba Tinubu ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin da yake shan ruwa da shugabannin addini da sarakuna a fadar gwamnati a Abuja, inda ya yaba da irin rawar da suke takawa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali da kyawawan halaye a tsakanin al’umma.
“Tabbas muna fuskantar ƙalubale. ‘Yan ta’adda suna cikin wani hali saboda ana kai musu samame ana murƙushe shi. Amma ina ba ku tabbacin abu ɗaya, Najeriya ba za ta miƙa wuya ba. Ba za mu sare ba. Za mu yi nasara,” in ji shugaban ƙsa.
Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin ci gaba da amfani da damar da yake da ita wajen jagorancin ƙasar nan ta hanyar tabbatar da bunƙasar tattalin arziƙi.
“Ina gode muku kan damar da kuka ba ni. Abin da zan iya yi shi ne ba ku tabbacin sauke nauyin da ke kaina. Zan iya cewa yanzu an samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi.”
“Ana samun ci gaba. ‘Yan fansho na samun kuɗinsu. Mun ceci Najeriya daga durƙushewa.
“Akwai babban ƙalubale a lokacin da muka karɓi mulki mulki. A yau, zan iya cewa da alfahari cewa mun tsira. Ba gwamna a Najeriya da ke gudu zuwa banki domin ya ranto kuɗi ya biya albashin ma’aikata,” in shugaban ƙasa.
Ya kuma jaddada aniyarsa ta mayar da hankali wajen zuba hannun jari a ɓangarori kamar na noma da ilimi domin barin abin tunawa ga waɗanda za su nan gaba.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya da ka da su cire tsammani, yana mai ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar tsaro da bunƙasar arziƙi ga kowa.
A yayin da yake magana, Etsu Nupe, Yahaya Abubakar, ya miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa kan gayyatarsu domin shan ruwa na shugabannin addinin Musulunci guda biyu wanda ke nuna haɗin kai.
Ya nemi taimakon ubangiji wajen samun zaman lafiya a ƙasar nan da nasarar shugaban ƙasa.
Sarkin Nupe, ne ya wakilci sarkin musulmi kuma shugaban majalisar ƙolin harkokin Musulunci na ƙasa, Sa’ad Abubakar.
Shugaban ƙungiyar Kiristoci na ƙasa (CAN), Archbishop Daniel Okoh, ya samu wakilcin Stephen Baba-Panya, shugaban Eɓangelical Church Winning All (ECWA), waɗanda suka bai wa shugaban ƙasa tabbacin mara wa gwamnatinsa baya a ƙoƙarin da take yi na kawo sauyi a fannin tattalin arziƙi da ƙarfafa tsaro a Najeriya.
Sakarakuna da malaman addini daga dukkan shiyyoyin ƙasar nan ne suka samu halartar taron buɗa bakin.
