Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga watan Maris da Juma’a 20 ga watan Maris 2026 a matsayin ranakun hutun bikin Eid al-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen watan azumin Ramadan. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar ga manema labarai a ranar Talata.
A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara. Ya kuma buƙaci Musulmi da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’u kamar soyayya, karamci, zaman lafiya, haƙuri da sadaukarwa da aka koyar a lokacin azumi.
Ministan ya kuma yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa. Ya jaddada muhimmancin zaman tare cikin lumana tsakanin al’umma daban-daban a ƙasar.
Haka kuma, gwamnati ta buƙaci jama’a da su yi bikin cikin natsuwa tare da taimakawa marasa galihu a cikin al’umma. Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya baki ɗaya.
