Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara bayan da suka ƙwato wasu littattafan sirri daga hannun mayaƙan ISWAP da aka kashe a yankin Mallam Fatori, jihar Borno, waɗanda ke nuna yadda ƙungiyar ke tsara hare-harenta da rarraba makamai.
Rahotanni sun nuna cewa littattafan sun ƙunshi jerin sunayen mayaƙan da aka tura domin kai hari, rawar da kowannensu zai taka, irin makaman da aka ba su, da kuma adadin harsasai da aka ware musu. Wannan na nuna irin tsari mai ƙarfi da ƙungiyar ke da shi wajen gudanar da ayyukanta.
Wani masanin harkokin tsaro, Brant Philip, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa irin wannan tsarin ya yi kama da abin da ake gani a sauran rassan irin waɗannam ƙungiyoyi a wasu ƙasashe, musamman a yankin Puntland na Somaliya.
A cewarsa, waɗannan littattafai na nuni da cewa ƙungiyar ba wai kawai tana kai hare-hare ba ne, har ma tana ƙoƙarin kafa tsari irin na gwamnati, inda take da nata ‘yan sanda, rundunar soja, ma’aikatu da sauran sassa na gudanarwa.
Masana tsaro na ganin cewa bayanan da ke cikin waɗannan littattafai za su taimaka matuƙa wajen gano yadda ƙungiyar ke tsara kai hare-hare, yadda take rarraba kayan aiki da kuma hanyoyin sadarwarta, wanda hakan zai ƙara bai wa jami’an tsaro damar dakile ayyukanta a nan gaba.
An tattaro waɗannan hujjoji ne daga wuraren da ƙungiyar ISWAP ta kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, wanda ya daɗe yana fama da matsalar tsaro.
