Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haka kuma gwamnan ya yabawa al’ummar jihar Katsina kan yadda suka nuna juriya, haƙuri da haɗin kai kan halin rashin tsaro a wasu sassan jihar.
Gwamnan na magana ne a wata hira da manema labarai jin kaɗan bayan tasowa daga Sallah a filin Eid na Ɓatagarawa a jihar Katsina.
Ya yabawa jami’an tsaro da iyayen al’umma kan rawar da suka taka wajan tabbatar da tsaro a jihar.
Malam Dikko Raɗɗa ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar,ya bayyana azumi watan Ramadan da bikin sallah a matsayin muhimmin lamari ga al’ummar Musulmi na duniya da ya kamata Musulmi su yi waiwaye da gode wa Allah da”ya bamu damar kai wa wannan lokacin.
“Wannan wata dama ce ga Musulmin Duniya a wannan lokaci da su ƙarfafa zumunci da son juna a tsakanin su,”Inji Mallam Dikko Raɗɗa.
A cewar sa darussan da aka koya a cikin watan Ramadan na tausaya wa, haƙuri da kyautatawa ya kamata Musulmi su cigaba da irin waɗannan abin alheri.
Gwamnan yayi fatan a shekara mai zuwa in Allah ya yadda Musulmi da sauran al’ummar jihar za su yi azumi Ramadan da Sallah cikin natsuwa da zaman lafiya.
