Daga ABUBAKAR A. BOLARI, Gombe
Tafarkin Gombe, Dakta Ibrahim Jalo Daudu, ya yaba matuƙa da yadda aka gudanar da bukukuwan sallar ƙarama cikin zaman lafiya da cikakken tsaro a faɗin Jihar Gombe. Ya ce bana sallah ta gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, ba tare da samun wani rahoton tashin hankali ko barazanar tsaro ba, lamarin da ya bayyana a matsayin babban abin alfahari ga gwamnati da al’ummar jihar baki ɗaya.
Dakta Jalo Daudu ya danganta wannan nasara da jajircewar Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa a dukkan sassan jihar.
A zantawarsa da wakilinmu a Gombe, ya bayyana cewa an gudanar da dukkan muhimman al’adun sallah da hawan sallah na kwanaki uku cikin tsari da lumana. Hakan ya haɗa da sallar Idi, hawan sallah, gaisuwar sallah a rana ta biyu, da kuma hawan Tudun Wada, ba tare da wata tangarɗa ba.
Ya ƙara da cewa irin wannan yanayi na zaman lafiya yana ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, tare da bunƙasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Tafarkin Gombe ya kuma jinjinawa Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, bisa yadda yake tafiyar da masarautarsa cikin hikima da adalci, yana haɗa kan al’umma manya da yara domin ƙarfafa haɗin kai.
Sai dai ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ƙoƙarin dusashe wasu al’adun gargajiya a jihar, musamman tashe da sauran wasannin gargajiya na Bahaushe.
A ƙarshe, Dakta Ibrahim Jalo Daudu ya yaba wa al’umma bisa yadda suke nuna ƙauna ga sarkinsu tare da ci gaba da yi masa addu’o’in alheri.
