Wayar Gawuna ta ƙi samuwa yayin da Tinubu ke ƙoƙarin hana shi bin tafiya Kwankwasiyya – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasir Yusuf Gawuna, ya zama jigon tattaunawar siyasa a Kano, yayin da ake zargin cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar umarni su dakatar da shirin sauya sheƙarsa zuwa tafiyar Kwankwasiyya, wadda daga bisani za ta iya kai shi jam’iyyar ADC.

Rahotanni sun nuna cewa shirin Gawuna na haɗa kai da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin ƙalubalantar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027, yana ƙara ɗaukar hankali a fagen siyasar jihar.

Wannan yunƙuri ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin APC, yayin da magoya bayan Kwankwasiyya ke nuna farin ciki da yiwuwar sauyin sheƙar.

A wani mataki da ya ƙara nuna kusanci da tafiyar Kwankwasiyya, wata tawaga ƙarƙashin jagorancin limamin masallacin gidan Gawuna, Malam Ahmed Sabo Usman, ta kai ziyarar Sallah ga Kwankwaso a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar APC sun bayyana cewa a kwanakin baya-bayan nan, Gawuna ya kasance ba ya samuwa ta waya, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa yana gudanar da muhimman shawarwari a ƙasashen waje. Duk ƙoƙarin da wasu manyan ’yan APC suka yi na tuntuɓarsa bai yi nasara ba.

Rahotanni sun ce Gawuna ya tafi ƙasar Saudiyya a watan Ramadan domin gudanar da Umrah, amma har bayan kammala azumin bai dawo gida ba. Wata majiya ta ce daga nan ya wuce wata ƙasa a Arewacin Afirka domin hutun sirri.

Haka kuma, an ce ya sanya wayarsa a yanayin “Do Not Disturb” domin kauce wa matsin lamba da yawan kiran waya daga shugabannin jam’iyyar da ke ƙoƙarin hana shi sauya sheƙa.

Wannan lamari ya jefa APC ta Kano cikin damuwa, har ta kai ga cewa Gwamna Abba Yusuf ya nemi taimakon Shugaban ƙasa domin shawo kan Gawuna kada ya bar jam’iyyar. 

Rahotanni sun ce an tura wani sanata mai tasiri daga Zamfara tare da wani mai ba shugaban ƙasa shawara domin jagorantar wannan yunƙuri.

A cewar wasu majiyoyi, APC na duba yiwuwar bai wa Gawuna tikitin takarar sanata kai tsaye a mazaɓar Kano ta Tsakiya a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar.

Masana siyasa na ganin cewa Gawuna na daga cikin ’yan takarar gwamna mafi ƙarfi a Kano, wanda zai iya kawo cikas ga duk wani tasirin gwamnati mai ci tare da raba ƙarfi a tsakanin APC. Sun kuma yi hasashen cewa haɗin gwiwarsa da Kwankwaso zai iya zama babbar barazana ga sauran ’yan takara.

Wani masani, Aminu Bashir, ya ce idan aka ba Gawuna tikitin gwamna a ƙarƙashin Kwankwaso, to zai zama “ƙarshen wasa”, ganin irin goyon bayan da yake da shi musamman a tsakanin matasa, malamai da ’yan kasuwa.

Sai dai kuma, wasu daga cikin jiga-jigan APC sun nuna rashin jin daɗi kan yadda ake zargin an ware Gawuna daga manyan muƙamai bayan zaɓen 2023, duk da irin ƙuri’un da ya samu. Wasu magoya bayansa na ganin an yi masa sakaci, musamman ganin cewa bai samu muhimman muƙamai a matakin tarayya ko cikin jam’iyya ba.

Har ila yau, akwai koke daga ɓƙngaren mabiyansa dangane da rashin biyan wasu haƙƙoƙinsa na tsohon mataimakin gwamna, duk da kiran da aka yi a baya na a biya irin waɗannan haƙƙoƙi.

By ukarofi