Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Bukuyum da ke Jihar Zamfara sun nuna cewar al’ummar yankin sun fuskanci wani samamen harin ‘yan bindiga a jiya Alhamis wanda ya yi sanadiyyar garkuwa da mutane sama da 15.
Mazauna yankunan sun ce ƙauyuka da dama ne ƴan bindigar suka tarwatsa, inda ɗaruruwan mutane suka yi gudun hijira zuwa garin Bukkuyum Shelkwatar ƙaramar hukumar ta Bukkuyum don tsira da rayuwar su.
Hon Sulaiman Abubakar Gumi, ɗan majalisar wakilai na tarayya mai wakilar Gumi da Bukkuyum ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mazauna ƙauyukan Kurfa Ɗanya da Kurfan Magaji sun fuskanci harin dayayi sanadin garkuwa da sama da mutum 150.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu duka mutanen waɗannan garuruwa sun gudu sun bar gidajensu, yayin da suke gudun hijira a cikin garin Bukuyyum.
Ya ci gaba da cewa yankin na ƙaramar hukumar Bukuyyum da Gumi da Anka ya jima yana fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Hon Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali domin magance matsalolin tsaron jihar ta Zamfara.
”Mun ga alamun gwamnati yanzu ta mayar da hankalinta a Borno, saboda barazanar dawowar Boko Haram, amma muna kira a gareta cewa Zamfara na fama da matsalar tsaro”, in ji shi.
Hakazalika duk ƙoƙarin da wakilin mu yayi don Jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar yaci tura a yayin haɗa wannan rahoton.
