Jihohi 21 sun gagara karɓar tallafin ilimi duk da matsalar yara marasa zuwa makaranta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A daidai lokacin da Nijeriya take fuskantar babbar matsalar taɓarɓarewar ilimi, wacce ƙungiyoyin raya ƙasa na duniya suka bayyana a matsayin ‘matsala mai buƙatar matakan gaggawa’, an gano cewa, sama da Naira biliyan 97 da aka ware, domin bunƙasa fannin ilimin bai-ɗaya sun kasance a banza ba tare da an yi amfani da su ba a jihohi da dama sakamakon yadda aƙalla jihohi 21 suka gaza karɓar tallafin.

Wannan lamari ya sake tayar da tambayoyi kan yadda ake tafiyar da mulki, aiwatar da manufofi, da kuma fifikon siyasa a ƙasar.

Binciken da shafin yaɗa labarai na Newspoint ya gudanar ya nuna cewa kuɗaɗen, waɗanda aka tanadar a ƙarƙashin tsarin tallafin ilimi na UBEC, sun kasa isa hannun jihohi da dama saboda gazawarsu wajen cika sharaɗin bada gudunmawar rabin kuɗin, wato counterpart funding.

A ƙarƙashin dokar ilimin bai-ɗaya ta shekarar 2004, Gwamnatin Tarayya na ba jihohi tallafi duk shekara domin inganta ilimin firamare da na sakandare. Sai dai dole ne kowace jiha ta bayar da kaso 50 cikin 100 na kuɗin da ake buƙata kafin ta samu damar karɓar tallafin. An kafa wannan tsari ne domin tabbatar da ɗaukar alhaki, gaskiya da ɗorewar ayyukan ilimi.

Sai dai takardun da aka samu ta hanyar dokar neman bayanai (Freedom of Information) sun nuna cewa zuwa watan Maris na 2026, aƙalla jihohi 21 da kuma Babban Birnin Tarayya sun kasa karɓar kuɗaɗen da aka ware musu.

Adadin kuɗaɗen da ba a taɓa su ba yanzu ya kai kusan naira biliyan 98, inda shekarar 2025 kaɗai ta samu mafi girman gazawa a tarihin shirin, da kusan naira biliyan 68.1 da aka bari babu wanda ya taɓa su a cikin shekara guda.

Masana harkar manufofin ilimi sun yi gargaɗi cewa wannan hali na nuna wata babbar matsalar shugabanci, inda ake kasa amfani da albarkatun da ke akwai wajen magance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni daga UNICEF da kuma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya suka nuna cewa kimanin yara miliyan 18.5 a Nijeriya ba sa zuwa makaranta — mafi girma a duniya. Nijeriya na ɗauke da kusan kashi ɗaya cikin biyar na yara marasa zuwa makaranta a faɗin duniya.

Rahoton ya kuma bayyana cewa matsalolin talauci, rashin tsaro, al’adu, ƙarancin kuɗin ilimi da kuma raunin shugabanci a matakin jihohi ne manyan abubuwan da ke haddasa wannan matsala.

Hukumar ta yi gargaɗi cewa rashin saka hannun jari cikin ilimi na iya jawo wata babbar matsala ga gaba ɗaya al’umma da tattalin arziki a nan gaba.

Abin lura shi ne, wasu jihohin da suka fi yawan kuɗaɗen da ba su karɓa ba ba lallai su ne mafi talauci ba, lamarin da ke nuna matsalar fifiko fiye da ƙarfin tattalin arziki.

Jihar Imo ce ke kan gaba da naira biliyan 10.6 da ba a karɓa ba, sai Ogun da naira biliyan 9.7, yayin da Ribas ke da naira biliyan 7.8. Sauran jihohin da suka biyo baya sun haɗa da Neja, Abiya da Oyo, kowannensu na da sama da naira biliyan 7.1 da aka bari babu amfani.

Haka kuma Babban Birnin Tarayya tana da naira biliyan 5.07 da ke zaman banza, yayin da Ekiti, Bayelsa da Adamawa ke da sama da naira biliyan 3.5 kowannensu.

Masana ci gaba sun bayyana wannan gazawa a matsayin wata matsala mai zurfi ta shugabanci a matakin jihohi.

Sai dai a gefe guda, akwai jihohi 15 da ke karɓar duk kuɗaɗen UBEC nasu ba tare da wata tangarɗa ba, abin da ke nuna cewa sharaɗin bada gudunmawar ba matsala ba ne idan an ba shi muhimmanci.

A yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da samar da kuɗaɗen, rashin iya ko rashin niyyar wasu jihohi wajen cika ƙa’idoji ya hana aiwatar da muhimman ayyukan ilimi kamar gina azuzuwa, ɗaukar malamai, samar da kayan koyo da inganta muhalli.

A halin yanzu da miliyoyin yara ke zaune a gida ba tare da makaranta ba, masana na gargaɗin cewa Nijeriya ba za ta iya jinkirta ɗaukar mataki ba.

Kamar yadda wata masaniya a fannin manufofi, Fatima Hassan Ibrahim, ta bayyana: matsalar ba wai rashin kuɗi ba ce, illa dai rashin amfani da kuɗin da ke akwai.

By ukarofi