
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne a Jihar Borno, sun farmaki ofisoshin ‘yan sanda guda biyu a Nganzai da ke Ƙaramar Hukumar Nganzai da Damsak a Ƙaramar Hukumar Mobbar.
A yayin harin, wanda ya auku a jiya Asabar, an ce mayaƙan sun harba ababen fashewa na gurnet da wasu muggan makamai, sannan sun yi damejin wani sashe na ofishin tare da ƙone wata motar yaƙin jami’ai da ta jima a ajiye.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Nahum Kenneth Daso ya bayyana haka a wata takarda a ranar Asabar, inda ya ce ‘yan sanda huɗu da wani mafarauci sun rasu a yayin harin.
Ya ce, tuni dai jami’an tsaro suka kai ɗauki a yanki tare da mayar wa maharan martani da dawo da zaman lafiya a yankunan.
A wani labarin kuwa, maharan sun farmaki sansanin ‘yan gudun hijira a yankin Malam Fatori da ke Damasak, inda suka farmaki jami’an haɗaka na CJTF da mafarauta da ke aiki a mashigar sansanin.
A farmakin ne wani mafarauci, Atom Abua mai shekaru 40 ya rasa ransa, yayin da kuma aka ƙone tantina da lalata kadarori masu yawa.
Kazalika, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Naziru Abdulmajid ya yaba wa jami’an bisa mayar da martani a lokacin da ya dace wajen hana mayaƙan karɓe iko da yankin.
Haka kuma, ya jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu a harin, yana mai tabbatar musu da cewa za a farauto masu hannu aciki tare da gurfanar da su a gaban doka.
A ƙarshe, ya roƙi al’umma da su cigaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen ba su bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wa ayyukan ba su tsaro.
