Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Spread the love

Daga FARFESA AHMAD MURTALA MANSUR

Ci gaba daga makon jiya.

6- A halin yanzu duk da waɗannan matsaloli, amma akwai ƙasashen da suka huwace amfani da Bitcoin kamar ƙasashe irin su Jamus, Ingila, Sweden, South Korea, Kuwait, Oman, Jordon, da sauransu. Wasu manyan kamfanonin manhajar kwafiyoyutoci da kafofin sadarwa irinsu Microsoft da Google da Yahoo duk sun karbi amfani da wannan kwandala ta Bitcoin. Haka nan wasu gidajen sayar da abinci da otel-otel duka sun yarda a biyasu ta hanyar amfani da ita. Takai ana sayan wasu tikitin na hawa jirgin sama da kudin Bitcoin. Sannan kuma an sami wasu jami’o’i kamar na Kasar Cyprus da suka yarda da a biyasu kudin makaranta da wannan kudi.

Duk da cewa kasar Jamus su ne suka fara yarda da tsarin mu’amallar Bitcoin, amma a zahiri bawai a matsayin kudi ba. Sai dai kurum a matsayin ksar ta sami wata dama da zata dorawa haraji ga manya da kananan kamfanonin da suke yin mu’amallar Bitcoin. Mutane kuma daidaiku aka barsu ba tare da wani abu ba. Don haka sun yarda da shi ne don samun kudin shiga kurum. 

A gefe guda kuma akwai kasashe masu yawa da suka hana amfani da Bitcoin kamar su Su’udiyya, Dubai, Turkiyya, Misra, Morocco, Algeriya, Lebanon, Russia, da sauransu. Babbabn Bankin Kasar China ya hana hulda da Bitcoin tun 2013. Suka dada daukar zafi wajen hana hulda da Bitcoin baki daya a 2017 da 2018.-(Everything You Need to Know about Bitcoin: Its Mysterious Origins and the Many Alleged Identities of Its Creators na Zoe Bernard, 2018)

7- Wannan ya kawomu ga yadda za a kalli mu’amalla da Bitcon a Musulunce. Akwai abubuwa da yawa da za a dubawa daki-daki don a fitar da hukunci da ya dace da yadda ake gudanar da Bitcoin a hain yanzu. Abin da malamai suka tsaya suna ta kokarin tantancewa shi ne dabi’ar wadannan kwaldalar ta Bitcoin shin ‘kudi’ ce ko kuwa ‘kadara’ ce? An sami wadanda suke kallon da fahimtar Bitcoin da daya daga cikin wadannan hanayoyi. A kan haka kuma suka fitar da hukuncinsu game da shi, wasu suka halatta, wasu suka haramta.- (The Shari’ah Factor in Cryptocurrencies and Tokens na Shari’ah Review Bureau a Kasar Bahrain; Shari’ah Analysis of Bitcoin, Cryptocurrency and Blockchain na Mufti Muhammad Abu-Bakar). Amma a gaskiya in an dubeta da kyau za a ga bata fada cikin ma’anar wani daga dayan abubuwan nan guda biyu ba. Haka nan yanayinta bai dace da yanayin kowane daya daga cikinsu ba.

i- Duk da cewa masu harkar Bitcoin suna amfani kalmomin da suke nuna kudi ne kamar ‘coin’ ko ‘currency’ da sauransu, amma a hakika ba kudi ba ne. Domin bai cika wasu daga cikin ka’idojin da Musulunci yake la’akari dasu a matsayin kudi ba. Wadannan sun hada da:

a- Sai gwamnati mai ci ta amince da wannan abu a matsayin kudi wanda duk mutane zasu rika mu’amalla da shi. Malaman Musulunci sun bayyana haka a fili. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa, “Ba wanda zai buga kudi sai gidan buga kudi (na gwamnati) da izinin shugaban. Saboda mutane in ka yi musu rangwame a kansa, sai su wuce gona da iri”. Sai Imamu Abu Ya’ala ya ce, “Imamu Ahmad ya hana a buga kudi ba tare da izinin shugaban ba saboda yin hakan wani ta’addanci ne gareshi”.—(Ahkamus Suldaniyyah na Abu Ya’ala: 181; Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/226; Annukud Wal-Bunuk Fin Nizamil Islami na Dr. Auf Muammad Al-Kafrawi:sh/20-56).

Imamu Nawawi shi ma ya yi bayanin cewa duk malaman Mazahabin Shafi’iyya ba su yada da wani ko wasu gungun mutane su ware su buga kudi ko su kirkiro wasu kudade daban ba wanda gwamnati ta yarda da shi ba. Ya ce, “Ana kin wanda ba shugaban ba ya buda kudi (kamr dinare da azurfa) ko da kuwa masu kyau ne sosai. Saboda buga kudade aikin shugaban ne. Sannan kuma ba za a aminci don za a iya samun algus da barna”.(Al-Majmu’u na Nawawi:6/11; Raudatud Dalibina na Nawawi:2/258).  

Wannan yana nuna cewa kamar yadda ba a son fito-na-fito da gwamnati a sha’anin mulki da gudanarwa, to haka nan ba a son a Musulunce keta alfarmar gwamnati wajen buga kudade ba tare da wani izini ba. Domin tsayuwa da daidaituwar kudi wata alama ce ta tabbatuwar gwamnati. Ibnu Khaldun ya yi bayanin cewa abubuwa guda biyu su ne ginshikan duk wata daula. Su ne karfi da kudi. Idan zata ruguje tana rugujewa ne da rygujewar wadannan wadannan abubuwa.-(Al-Mukaddimah na Ibnu Khldun: sh/294) 

A nan Nigeriya, dokokin Kasa sun hana amfani da Bitcoin da hulda da shi. A 17 na Janairu na 2017 Babban Banki Kasa (CBN) ya haramta amfani da shi ta kowace fuska. Ma;anar wannan da a ce za asami wani yake wani kar da sunan ya rike masa kudi ta hanyar Bitcoin, ba za a saurari karar ba. Saboda ba ta sabawa dokin kasa.

Sai dai yana da kyau a sani cewa, a zamani irin wannan ba wai yarda ko rashin yardar wata kasa kadai shi ne abin la’akari wajen halatta wani abu ko haramtashi ba. Saboda a yanzu kasashe sun yarda da tsarin banki mai ruwa, amma wannan bai sa an ce shi kenan yin hakan ya halatta ba. A lokacin da Daular Musulunci take da karfi da iko, ana gudanar da abubuwa a kan Shariar Allah, a lokacin ana iya cewa ba laifi ana iya laakari da wasu abubuwan saboda gwamnati ta yarda shi. Amma ko a da can har da kuma yanzu, ana duba yadda abu yake cikinsa-da-bayansa, sannan sai malamai su bada fatawa da zata bayyana matsayinsa a Shari’a na halasci ko haramci. Wannan wani abin dubawa ne da kyau.   

b- Bayan gwamnati ta yarda da duk abin da take ganin za iya tsayawa a matsayin kudi, za a ga duk mutane sun yarda da su a mu’amalolinsu na yau-da-gobe. Wannan shi ne abin da Imamu Malik yana cewa, “Da a ce mutane zasu yarda da fatun dabbobi a tsakaninsu a bugasu a matsayin kudade, da ba zan so a sami jinkiri ba idan sun yi canja fata da dinare da azurfa”.-(Al-Mudawwanah: 3/5. A dada duba ra’ayin Hanafiyya a Littafin Tanbihur Rukud Ala Ahkamiln Nukud na Ibnu Ibidn: sh/25).”

Ma’anar maganarsa ita ce duk abin da mutane suka hadu a kan cewa kudi ne, kuma suka gina rayuwarsu a kansa, ya zama kudi. Duk hukunce-hukuncen Shari’a na kudi zasu shafeshi. Kudi suna da sifar zamowa tsanin da kowa-da-kowa zai yi amfani da shi wajen  saye-da –sayarwa. Ba a la’akari da kudaden da suka zamo masu gudanawa tsakanin wasu tsurarun mutane.-(Al-Warkun Nakadi na Sheikh Abdullah bn Mani’i sh/17). Bitcoin ba kudi ba ne da kowa-da-kowa yake da ikon amfani da su cikin sauki ba. Kudade ne-in har an yarda ma cewa kudin ne-da suke yawa a kan internet kurum. Wadanda suke huldar su kadai suka san da su, kunzumin mutane ba su da alaka da wadannan kudaden na boye!

c- Kudi abu ne na zahiri da yake zamowa ma’aunin kimar abubuwa a fadin duniya, ta yadda abin da aka saya ya zamo daidai da kimar kudin da a ka sayeshi da su.-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 5/419). Don haka ne ake da kudi kala biyu:

Na ɗaya: Abubuwan da su da kansu kudade ne kamar gwal da azurfa. Har yanzu ana daukar gwal cikin manyan abubuwan da kasashe suke ajiyewa a matsayin (Foreign Exchange Reserve). 

Na biyu: Abubuwan da gwamnati ta yarda da su a matsayin kudade kamar takardun kudi na Naira, Riyal, Dollar, Euro da sauransu. Tuntuni Malamai suka tabbatar da karbar takardun kudi. Kafin wannan zamanin ma Imamu Malik ya fadi maganar da aka kawo a sama. Har ila yau kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyyah shi ma ya yi bayanin da za a dora takardun kudi a kansa. Ya ce, “Dinare da azurfa ba su da wata wani iyaka ta al’ada ko ta Shari’a. Makomar lamarinsu bata wuce al’ada da abin da mutane suka yarda da shi a tsakaninsu. Saboda su kudi tun asali ba manufarsu kenan ba. Manufar it ace su zamo ma’auni na abubuwan da ake mu’amalla da su kurum. Dinare da Dirhami ba su da kansu ne manufa ba. A na daukarsu ne a matsayin tsani kurum don a yi mu’amalla da su. Don haka ne ma suka zamo kudade, sabanin sauran dukiya, wadanda asalin manufar samuwarsu ita ce a yi amfani da su”-(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyyah: 19/251).

Manufar kawo wannan don a nuna cewa Bitcoin bai sami irin wannan darajar ta karbuwa a matsayin kudi ba a kasashe da yawa ba. Abin da yake faruwa dangane da shi shi ne wani mutum ko wasu mutane ne kurum suka kirkireshi a kan internet, sannan tsakanin duhun-dare da sanyin-safiya suka bace aka kasa ma gano ko waye har yanzu! 

d- Sannan kuma ana biyan kudade idan wani ya salwantar da su. Ita kuwa kwandalar Bitcoin, in ta salwanta, ba mai biya ko ya dawo da ita. Don haka ciniki da hulda da ita ya shiga haramci saboda garari da hadarin da yake ciki. 

e- Bitcoin ya fi kama da kudin-ganye (Alfulus): Ana kirkirar kudin ganye ne saboda dalilai da yawa, musamman don a shirgar da su cikin mutane su bada mai kyau a basu mara kyau. Ibnul Kayyim ya yi bayani mai gamsarwa a kan yanayin kudin-ganye. Idan aka yi la’akari da bayaninsa a kan Bitcoin za a ga kamannin ya bayyana sosai. Ya ce, “Kamar yadda ka gani dangane da rugujewar mu’amallar mutane da irin cutuwa da tale samunsu idan suka fara amfani da kudin-ganye (Alfulus) a matsayin kadara don samun riba. Yin haka sai ya kawao cutuwa da zata game ko’ina, zalunci ya yadu. Da an daukesu a matsayin kudi na-bai-daya, baya karuwa ko ya ragu, wanda zai zamo ma’unin abubuwa, amma ba a auna shi da kadarori, da an yi haka da lamarin mutane ya gyaru…Saboda ba a burin samun kudi su a karan-kansu, sai dai ana bukatarsu ne don akai ga sayan kadara/haja. Idan kudade su da kansu suka zamo kadara, ana hankoron a samesu kamar kadara, sai lamarin mutane ya lalace. Wannan bayani ne na hankali da ya shafi zallan kudi, ba zai tsallaka zuwa wasu Abubuwan ba”.-(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/156-157).

Malamai irinssu Imamu Gazali suna fada cewa, “Idan kudin-ganye suka sami karbuwa kamar kyawawan kudade, to sai su zamo kamar kadara, a maganar malamai mafi inganci”- (Nuzhatun Nufusi Fi Bayani Hukumit Ta’amuli Bil Fulusi na Ibul Ha’imi Ahamd bn Muhammad, sh/47)

 ii- Duk da cewa Bitcoin ya so ya yi kama da ‘kadara/haja’ (Legit commodity/goods) amma ba kadarar ba ce. Domin ita kadara/haja tana zamowa a hannu sannan ta biyawa wanda yake da ita wata bukata ta musamman kamar ya sa a cikinsa ko ci ko ya sha ko ya shiga in gida ne ko ya hau kamar mota ko keke da doki da sauransu. Haka nan kadara tana samun kula ta wajen tabbatar da kyau da tsari daga hukumomi. Bitcoin kuwa bata da irin wadannan sifofi. Saboda Bitcoin tna gujewa hukumomi. Sannan kuma iyakacinta kan internet ba kari. Shi ya sa bai dace ba a dauketa a matsayin kadara har kuma a gina hukunci na halaccin tsarin bakidaya a kan haka.

Ci gaba a makon gobe insha Allahu.

Farfesa Ahmad Mansur shine tsohon Shugaban Sashen Addinin Musulunci na Jami’ar Bayero

By ukarofi