Jagororin ADC da PDP sun sa labule a Abuja bayan zanga-zangar adawa da matakin INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyun PDP da ADC sun shiga wani taron gaggawa domin tattaunawa kan matsalolin da jam’iyyun adawa ke fuskanta.

Taron, wanda ke gudana a Abuja ya samun halartar manyan jagororin jam’iyyun, wanda suka haɗa da Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, David Mark da Peter Obi.

Sauran sun haɗa da Abubakar Malami; Babachir Lawal; Rotimi Amaechi; da kuma Sanata Aminu Tambuwal.

Haka kuma, akwai Seyi Makinde; Kabiru Tanimu Turaki; Farfesa Jerry Gana; Adolphus Wabara; da kuma Babangida Aliyu.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke cigaba da zargin gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC na haddasa musu rikici wajen yin amfani da hukumomin ƙasar.

By Babaji