Ka dawo gida – Shugaban APC ya roƙi Shekarau ya dawo jam’iyyar yayin ziyartar sa a Kano

Spread the love

Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kai wata muhimmiyar ziyara a Kano domin tattaunawa da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, da kuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo.

Ziyarar ta gudana ne a gidansa Shekarau da aka fi sani da Mundubawa Palace, inda ake ganin matakin wani yunkuri ne na APC na jawo manyan ‘yan siyasa yayin da ake fuskantar sauye-sauyen kawance kafin zabuka masu zuwa.

A yayin ganawar, shugaban APCn ya roƙi Shekarau da Gwarzo da su koma jam’iyyar, yana mai bayyana kansa a matsayin ɗansu da ke neman shiriya da goyon baya.

Har ila yau, ya buƙaci sauran magoya baya da ke wurin su taimaka wajen lallashin shugabannin domin su dawo APC, yana jaddada muhimmancin haɗin kai musamman a Arewacin Nijeriya.

A nasa jawabin, Sanata Shekarau ya yaba da yadda shugaban APC ya kai ziyarar da kansa, yana mai cewa hakan alama ce ta girmamawa da muhimmancin batun.

Ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da shi da abokan siyasarsa ke duba makomar su, musamman duba da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shekarau ya bayyana cewa duk wata shawara da za su dauka za ta dogara ne da abin da ya fi anfani ga jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa Shekarau na dab da ficewa daga PDP, amma ya nuna ba zai shiga wata sabuwar jam’iyya kamar ADC ba.

A lokaci guda kuma, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai masa ziyara kwanaki uku da suka gabata, sannan daga bisani ya gana da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, alamar yadda siyasar jihar ke ƙara ɗaukar wani sabon salo.

By Babaji