Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP ne sun kai wani mummunan hari da tsakar dare a garin Benisheikh da ke ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno, inda suka hallaka wani babban jami’in rundunar soji, Birgediya Janar O. O. Braimah.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya kasance kwamandan rundunar haɗin gwiwa a yankin, kuma ya rasu ne yayin da yake jagorantar dakarunsa a fafatawar da suka yi da maharan.
Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Alhamis, a wani salo na hare-hare da aka shirya a lokaci guda a wurare da dama, ciki har da Benisheikh da kuma al’ummar Pulka da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
An ce bayan ɓarkewar yaƙi, an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin dakarun soji da ’yan ta’addan, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula, wasu jami’an tsaro, membobin rundunar sa-kai ta Ciɓilian Joint Task Force, da kuma ɗimbin ’yan ta’adda.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shigo garin Benisheikh cikin dare, inda suka banka wa manyan motoci da sauran ababen hawa wuta, tare da lalata kadarori masu yawa.
Lamarin ya ƙara muni sakamakon kasancewar matafiya da dama a garin, waɗanda suka maƙale a Benisheikh sakamakon rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da ake yi da yamma domin dalilan tsaro.
A yayin artabun, Birgediya Janar Braimah ya rasa ransa yana jagorantar dakarun sa, yayin da sojoji suka yi nasarar kashe ’yan ta’adda da dama.
Wani mazaunin yankin, Malam Lawal Benesheikh, ya bayyana alhini kan lamarin, inda ya ce wannan hari babban rashi ne ga rundunar soji da ma al’ummar yankin baki ɗaya.
Bincike ya nuna cewa jerin hare-haren ya fara ne tun daren Laraba a garuruwan Pulka da Bakin Ruwa, inda maharan suka kai hari kan sansanonin soji, suka lalata kayan yaƙi da kuma wasu muhimman kayayyaki.
Haka kuma an ruwaito cewa maharan sun sake kai wani hari a Benisheikh da Ngamdu, inda suka kwace iko da sansanin rundunar 29 Task Force Brigade, tare da ƙona motoci da kayan aikin soji.
A Pulka kuwa, an ce ’yan ta’addan sun kwashe kayan abinci daga shaguna tare da lalata wasu muhimman kayayyaki, ciki har da na kamfanin da ke aikin gina hanya a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa garin Pulka na ɗauke da dubban ’yan gudun hijira daga Ngoshe, wazanda suka tsere daga muhallansu bayan wani hari da Boko Haram suka kai kimanin wata guda da ya gabata.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar Operation HADIN KAI a shiyyar Arewa maso Gabas ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da waɗannan hare-hare.
