Daga JOHN D. WADA Keffi
Ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar PDP Dr. David Martins Umbugadu ya yaba wa cocin Grace Baptist Church da ke Sabon-gari a karamar hukumar Keffi a jihar dangane da jajircewa wajen yaɗa bisharar Isa Almasihu cikin shekaru 15 da kafuwar cocin.
Dr. David Umbugadu ya bayyana haka ne ta bakin wani na kusa dashi maisuna Samurai Danjuma da ya wakilceshi a wajen wani babban bikin cika shekaru 15 da kuma neman tallafin naira miliyan 40 da cocin ya gudanar don kammala aikin gininta wanda aka yi jiya Asabar a cocin.
Yace dole ne a yaba wa cocin Grace Baptist church din don duk da ƙalubalai daban-daban da suka fuskanta a cikin shekaru 15 din basu karaya ba sun cigaba da gudanar da ayukan daukaka sunar Ubangiji.
Dr. Umbugadu bayan ya taya su murnar bikin cika shekaru 15 din ya kuma yi amfani da damar inda ya godewa shugaban cocin wanda shine kuma shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN a ƙaramar hukumar Keffi, Rev. Kefas Musa da sauran mambobin cocin baki ɗaya game da yadda suke fito ƙwansu da kwarkwata suke mara masa baya a duk lokaci da ya fito takarar gwamnan jihar inda yace Allah ne kawai zai saka musu.
Daganan sai ɗan siyasar David Umbugadu yayi alƙawarin tallafawa ikilisiyar daidai gwargwado musamman idan Allah ya bashi nasarar zama gwamnan jihar a zaɓen 2027 dake tafe kana yayi kira ga ‘yan uwansa ‘yan siyasa da masu hannu da shuni su tallafawa ƙoƙarin cocin wajen yaɗa aikin Allah.
Shima anasa ɓangaren da yake jawabi mamba dake wakiltar Keffi ta Kudu a majalisar dokokin jihar Hon. John Ovye shima ya jinjinawa aiki tukuru da cocin Grace Baptist church ɗin ta yi a cikin shekaru 15 din inda yace ba ƙaramin sadaukarwa shugabaninsu ke yi ta wannan fanni ba.
Yace baya ga hakan kasancewar shugaban cocin shine kuma shugaban ƙungiyar CAN a ƙaramar hukumar yana cigaba da hada kawunan kiristoci baki ɗaya duk da banbance-banbancen su ta cocin kana ya buƙaci sauran mujami’ai suyi koyi da cocin.
Daganan zai ɗan majalisar shima ya taya su murnar bikin kana yayi alƙawarin cigaba da yin duka mai yuwa wajen tallafawa cocin musamman idan ya samu matsayi mafi girma nan gaba.
Da yake gabatar da ƙasida na musamman a matsayinsa na babban baƙo mai jawabi a wajen bikin Rev, Sabonyaro D. Adams (rtd) bayan ya yaba wa ikilisiyar dangane da gagaruman nasarori da suka cimma zuwa yanzu ya kuma ƙalubalanci masu hannu da shuni cikin al’umma musamman kiristoci su riƙa zuba jari a ayuka da za su ɗaukaka sunar Allah maimakon duniya don ranar gobe ƙiyama Allah zai tambayi kowa game da yadda yayi amfani da dukiyar da ya bashi.
Yace tabbas idan aka kammala ayukan ginin cocin hakan zai taimaka matuƙa wajen faɗaɗa bisharar Ubangiji.
Shima a nasa ɓangaren shugaban cocin Grace Baptist Church Sabon Gari din Rev. Kefas Musa kuma shugaban ƙungiyar CAN a ƙaramar hukumar Keffi ya bayyana wa wakilinmu ta wani zantawa na musamman da ya yi da shi cewa cocin ta cimma nasarori da dama a cikin waɗannan shekaru 15 a fanin idar da salon Ubangiji da haɗa kan mambobin ta inda yace sun yanke shawarar faɗaɗa ginim ikilisiyar ne tare da rufe saman ginin kasancewar a yanzu ana gab da shiga damina.
Ya godewa duka waɗanda suka halarci taron suka kuma bayar da nasu tallafi tare da yin addu’ar Allah ya koma da kowa gida lafiya.
A ƙarshe shima shugaban kwamitin shirye-shiryen babban bikin Kwamaret Peter Theophilus Ewu ya jaddada cewa ikilisiyar ta shirya bikin ne don neman tallafi gun jama’a don basu damar rufe ginin cocin inda ya ƙara da cewa akwai babban lada ta musamman daga Ubangiji ga duk wanda ya bada gudumawa ga ire-iren ayukan addini irin wannan kana ya taya duka mambobin cocin murnar cika shekaru 15 din.
