Gwamna Sule ya yi wa ɗaliban NSUK 82 da aka yaye ruwan Naira

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Keffi

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya yi wa ɗaliban babban jami’ar jihar su 82 da suka kammala karatunsu suka kuma fito da satificate mai darajar farko ruwan naira inda kowannensu ya samu rabin miliyan sa’anan ɗalibai uku da su ka yi zara cikin ɗaliban sun samu miliyan daya kowanne.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa jami’ar ta tabbatar da bajintar ta na kasancewa ɗaya daga cikin manyan makarantun ƙasar nan da ake alfahari da su.

Ya bayyana haka ne a wajen taron yaye tsofin ɗaliban jami’ar karo na 8 da kuma cikar jami’ar shekaru 25 a ƙarshen mako da ya gabata a birnin Keffi.

Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana godewarsa na musamman ga shugaban jami’ar Farfesa Atahiru Jega da mai martaba sarkin Keffi Dr. Shehu Chindo Yamusa na lll da shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman game da nuna halin dattaku da ƙwarewa da kuma riƙon amana wajen inganta harkokin jami’ar da darajarta a duniya baki ɗaya inda ya ƙara da cewa wannan shine karon farko da babban jami’a irin wannan ya yaye manyan ɗalibai masu digiri digirhir a tarihin jami’oin ƙasar nan gaba ɗaya.

Gwamnan ya kuma yaba wa gagaruman gudumawa da ƙungiyar tsofin ɗaliban jami’ar da sauran abokan hulɗar jami’ar suka daɗe suna bayarwa wajen sauƙaƙa harkokin jami’ar inda ya buƙaci su cigaba da hakan.

Shima da yake jawabi babban shugaban jami’ar ta jihar Nasarawa Farfesa Attahiru Muhammadu Jega ya yaba wa shugaban jami’ar na farko wanda aka kafa jami’ar dashi wato Farfesa Adamu Baikie game da himmarsa da kuma sadaukarwa da yayi tayi har a a yau haƙar nasa ta cimma ruwa ta kafa tubalin duka waɗannan nasarori da ake samu a jami’ar a yanzu inda yace jami’ar ba zata manta da shi ba.

Farfesa Jega ya kuma yi kira na musamman ga gwamnatoci a duka matakai su cigaba da zuba jari a jami’ar don inganta harkokin karatu da cigaba a jami’ar inda ya yaba wa ƙoƙarin gwamna Abdullahi Sule a wannan fanni.

A nata jawabin na musamman shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta bayyana wasu daga cikin ɗimbin nasarori da jami’ar ta cimma a ƙarshen jagorancinta kawo yanzu inda ta buƙaci hukumomi da ƙungiyoyi daban-daban su cigaba da haɗa kai da jami’ar don ɗaurewar waɗannan nasarori.

Wakilinmu ya kuma rubuto cewa sama da waɗannan ɗaliban jami’ar dubu 30 ne aka yaye ayayin taron tare da basu takardar shedar kammala karatunsu, kana tun farko kafin taron gwamnan jihar ya kaddamar da wasu ayyuka da gine-gine da akayi a jami’ar da suka haɗa da sabon ƙaramin ƙofar shiga jami’ar da wajen taro da sabbin hanyoyi da sauransu tare da karrama wasu manyan shugabanni ciki har da shugabar ƙasar Tanzania da sauran su.

By ukarofi