2027: Burin Atiku na tsaya wa takara shure-shure ne da baya hana mutuwa, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana burin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar na tsaya wa takara a 2027 a matsayin shure-shuren da baya hana mutuwa bayan wani rashin kataɓus a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin.

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan harkar yaɗa labarai, Suday Dare ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce hirar da aka yi da Atiku ta nuna rashin hangen nesa da shirin shugabanci a matakin ƙasa daga tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

A cewarsa, ‘yan Nijeriyar da suka kalli hirar ba su samu gamsassun bayanai ba akan shugabanci ko alƙiblar tsare-tsare, a madadin haka an samu cin karo da juna a bayanan nasa da rashin makama game da sha’anin ƙasa.

Sunday Dare ya ce a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke ƙoƙarin daidaita al’amuran tattalin arziƙi ta gyare-gyaren da ya ɓullo da su, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gaza samar da mafita mai nagarta ko ɗaya.

Ya kuma soki watsi da gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ke yi da Atikun ya yi, inda ya bayyana shi a matsayin suka babu dalili wanda ke nuna zallar ƙiyayya a madadin shugabanci.

Haka kuma, ya zargi Atiku Abubakar da ware wasu ɓangarori a bayanansa, yana mai cewa hirar ba ta da armashi ko alƙiblar da aka gina ta a kai.

By Babaji