Tsohon tsarin haraji ne ya talauta Nijeriya – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa tsoffin dokokin haraji da aka gada tun zamanin mulkin mallaka sun taka rawar gani wajen talauta ’yan Nijeriya, sakamakon rikice-rikice, yawaitar dokoki da rashin daidaito da suka dabaibaye tsarin tattara kuɗaɗen shiga.

Shugaban ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin ƙaddamar da sabon babban ginin hedikwatar Hukumar Haraji (NRS) mai hawa 16, inda ya jaddada cewa sabbin gyare-gyaren haraji da gwamnatinsa ta ɓullo da su za su samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tsarin tattalin arziki mai amfani ga kowa.

A cewarsa, sabbin dokokin harajin da suka fara aiki a watan Janairu, an tsara su ne domin kawar da tsoffin matsalolin tsarin kuɗaɗen shiga, tare da mayar da Nijeriya ƙasa mai gasa a matakin duniya.

“Tun ranar rantsar da ni, na yi alƙawarin fitar da ’yan Nijeriya daga duhun rashin tabbas zuwa hasken sabon fata. Wannan ba magana ce kawai ba, alƙawari ne da muka ɗauka domin gyara tattalin arzikin ƙasa,” inji shi.

Shugaban ya yabawa Shugaban Hukumar NRS, Zacch Adedeji, bisa kammala aikin ginin cikin watanni 30 kacal, bayan sama da shekaru 20 ana jinkirta shi. Ya ce sabon ginin zai samar da yanayi mai kyau ga ma’aikata sama da 3,000, tare da kayan aiki na zamani da suka haɗa da cibiyar sarrafa bayanai, ɗakin horaswa, asibiti da sauransu.

Ya ƙara da cewa ƙaddamar da ginin ba wai kawai buɗe sabon ofishi ba ne, illa wata alama ce ta sake gina amincewa da inganta cibiyoyin gwamnati, musamman a ɓangaren tattara kuɗaɗen shiga.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri da manufofin gyaran tattalin arziki, yana mai cewa alamu sun fara bayyana.

Shi ma Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce sabbin gyare-gyaren sun kawo daidaito da tsari a cikin dokokin haraji da suka daɗe suna cike da ruɗani.

A nasa ɓangaren, Shugaban NRS, Zacch Adedeji, ya bayyana cewa an sauƙaƙa sama da dokokin haraji 60 zuwa tsarin guda mai ma’ana, yana mai cewa kuɗaɗen shiga sun ƙaru daga Naira tiriliyan 6.8 zuwa tiriliyan 28.7 a shekarar 2025.

Ya ƙara da cewa, waɗannan sauye-sauyen ba wai ƙarin haraji ba ne, illa inganta tsarin yadda ake tattarawa da sarrafa kuɗaɗen shiga domin amfanin jama’a.

Masana tattalin arziki na ganin cewa duk da kalubalen da ke tattare da sabbin tsare-tsaren, gyaran haraji na iya zama wata muhimmiyar hanya ta ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya, idan aka aiwatar da su yadda ya kamata tare da gaskiya da riƙon amana.

By ukarofi