Amurka da Iran na shirin komawa teburin tattaunawa duk da killace tashoshin jiragen ruwa

Spread the love

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran na iya sake farawa a ƙasar Pakistan cikin kwanaki biyu masu zuwa, kamar yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana, bayan da zaman sulhun ƙarshen mako ya rushe, abin da ya sa Amurka ta ɗauki matakin killace tashoshin jiragen ruwan Iran.

Jami’an diflomasiyya daga Pakistan, Iran da ƙasashen yankin Gulf sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar tawagogin Amurka da Iran za su koma Pakistan nan da ƙarshen wannan mako domin ci gaba da tattaunawa, duk da cewa wani babban jami’in Iran ya ce har yanzu ba a tsaida takamaiman ranar ba.

Trump, a wata hira da jaridar New York Post, ya ce akwai yiwuwar samun wani babban ci gaba cikin kwanaki biyu masu zuwa, yana mai kira ga masu sa ido da su kasance cikin shiri.

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya bayyana cewa Trump na neman cimma wata “babbar yarjejeniya” da Iran, amma ya jaddada cewa akwai babban rashin yarda tsakanin ƙasashen biyu, wanda ba zai warware cikin gaggawa ba.

Duk da zafafan kalamai daga Iran kan killacewar tashoshin jiragen ruwanta, alamun cewa tattaunawa na iya ci gaba sun taimaka wajen kwantar da hankalin kasuwannin mai, inda farashin gangar mai ya faɗi ƙasa da dala 100.

Tun bayan fara yaƙin a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta rufe mashigar Hormuz Strait, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas a duniya. Rikicin ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 5,000.

Tattaunawar da aka yi a Islamabad a ƙarshen mako bai haifar da yarjejeniya ba, abin da ya jefa makomar tsagaita wuta na makonni biyu cikin shakku, duk da cewa har yanzu akwai sauran mako guda kafin karewar wa’adin.

Babban abin da ya tsaya a gaba shi ne shirin nukiliyar Iran. Amurka ta buƙaci Iran ta dakatar da duk wani aikin nukiliya na tsawon shekaru 20, yayin da Iran ke son a rage wannan zuwa shekaru 3 zuwa 5.

Har ila yau, Amurka na matsa lamba a fitar da duk wani abu mai ɗauke da sinadarin nukiliya daga Iran. Duk da haka, wasu majiyoyi sun ce tattaunawar sirri da aka yi bayan zaman makon jiya ta nuna an samu ci gaba wajen kusantar juna.

Sai dai har yanzu ba a san irin yarjejeniyar da za a iya cimma cikin gaggawa ba, la’akari da wahalar yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 wadda Trump ya janye daga cikinta a 2018, tare da buƙatar sanya ido daga Hukumar Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Iran kuma na neman a ɗage mata takunkumin ƙasa da ƙasa, abin da Amurka ba za ta iya yi ita kaɗai ba.

Rundunar sojin Amurka ta ce babu wani jirgin ruwa da ya tsallake killacewar a cikin awanni 24 na farko, yayin da jiragen kasuwanci shida suka janye.

Sai dai bayanan zirga-zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa tasirin killacewar bai yi ƙarfi sosai ba, inda akalla jiragen ruwa takwas suka wuce mashigar Hormuz a ranar Talata.

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya rage hasashen bunƙasar tattalin arziki, yana gargadin cewa duniya na iya faɗa wa cikin koma bayan tattalin arziki idan rikicin ya tsananta kuma farashin mai ya ci gaba da kasancewa sama da dala 100.

ƙasashen Turai kamar Birtaniya da Faransa sun ce ba za su shiga cikin rikicin ba, duk da cewa suna iya taimakawa wajen tsaron mashigar idan an cimma yarjejeniya.

A gefe guda, Chana ta soki matakin Amurka, tana mai cewa yana da haɗari kuma zai ƙara tsananta rikicin.

A wani ɓangare, hare-haren Isra’ila a Lebanon na ci gaba, musamman kan ƙungiyar Hezbollah da Iran ke mara wa baya.

A Washington, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya jagoranci wata ganawa tsakanin wakilan Isra’ila da Lebanon, irinta ta farko tun 1993.

Lebanon na neman tsagaita wuta bayan hare-haren da suka kashe sama da mutane 2,000 tare da raba miliyan 1.2 da muhallansu, yayin da Isra’ila ke matsa lamba a kwance ɗamarar Hezbollah.

A halin yanzu, yaƙin bai samu karɓuwa sosai a cikin Amurka ba, inda wani bincike ya nuna kashi 35% ne kawai ke goyon bayan hare-haren Amurka kan Iran.

By ukarofi