Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Na ga wasu na rubuta wai ana yaƙi da masu kafa ƙungiyar Hausa zalla wanda sam-sam ba haka ba ne. Shin an kafa ƙungiyar ko har yanzu shiri a ke yi? Idan an kafa to me ƙorafin? In kuma shirin kafawa a ke yi wa ya rike wani ya hana shi kafawa? Mutane ne daban-daban kuma ko ƙungiyar za su kafa ba zai taɓa yiwuwa su kafa guda ɗaya ba. Yanzu ma haka su na nan su na cin zarafin juna don ba wani Bahaushe ko mutumin kirki da duniya ta sani a cikin su. Gara ma wani mutum a Kano da kan ziyarci wasu ‘yan ƙauyuka a Kano ya na taruka da kauyawa su faɗi abin da su ka ga dama a yayata a soshiyal midiya. Shi din ma don rashin zafin dokokin Nijeriya ne da wallahi bai isa ya ce shi shugaban ƙungiyar Hausa zalla ba ne. Na sha nunawa yaudarar hukumar yi wa kamfanoni rejista CAC da ya yi da rubuta gidauniyar tallafawa Hausawa ya ke son kafawa ba HAUSA ZALLA ba kuma a haka a ka yi ma sa rejista. Babu inda a rejistar a ka ba shi hurumin zagin kasuwa, habaici ko zayyana mai alfarma Sarkin Musulmi a matsayin Sarkin Fulanin Sokoto, rashin kunya ne. Kuma ba shi da hurumi a rejistar na yin taruka a kauyuka a kan lamuran tsaro ko magana a madadin Hausawa ko cin zarafin mutane da kalamai na rashin mutunci. Babu wanda ya ba shi hurumin nan kuma duk wani Bahaushe da ya ma ka shi a kotu cewa ba shi da hurumin magana a madadinsa za a bi ma sa haƙƙinsa.
Ita fa wannan ƙungiya mai taken “ƙungiyar Hausawan Nijeriya” haramtacciya ce kuma rejistar da a ka yi a 2022 ba da wannan ƙa’ida a ka yi ba balle ma a je ga shiriritar Hausa zalla. Babu wata ƙungiya a hukumance Hausa zalla amma haka shi mai iƙirarin shugabancin ƙungiyar ke rubutawa ko kunya ba ya ji kuma wallahi babu wani tabbaci da ke tabbatar da Bahaushe ne. Ko yanayin furucin bakinsa ba irin na Hausawa ba ne. Kai harshen turancinsa ma irin na kudu ne. Abu mai sauki ma karanta sunan kungiyar ta sa daidai ma ba zai iya ba ballanta har wai ya jagoranci Hausawan Nijeriya. Rubutun Hausa mai ma’ana ma da ke nuna sanin darajar harshen bai iya ba. Rejistarsa ba ta ba shi hurumin daukar membobi da kan rufe shafinsu a yanar gizo da amfani da sunayen karya su na zagin manyan magabatan musulmi da ruruta fitinar ƙabilanci ba. Bai taɓa fitowa ya barranta da membobinsa masu zunduma ashar da tallata manyan bindigogi da yin kira a ɗau makami ba.
Kazalika na ga wasu na kawo batun ƙungiyoyin makiyaya da akasarinsu Fulani ne da nuna wai ba a sukar kafa su. In ka ɗebe MIYETTI ALLAH MACBAN da ke matsayin ƙungiyar farko ta makiyaya “Cattle Breeders Association” duk sauran ‘yan ƙananan ƙungiyoyi ne da wasunsu ma bai fi mutum 10 ba ne daga shugabannin har membobi. An taɓa wani taro a Abuja a zamanin marigayi shugaba Umaru ‘Yar’adua inda a ka nemi a rushe dukkan ƙungiyoyin makiyaya su koma ƙarƙashin MACBAN. Tabbas duk wata ƙungiyar Fulani makiyaya da kowane suna, kan muradun makiyaya ne da ke zama a ruga amma ba ta ƙabilar Fulani ba. Ko TABITAL FULAKU na aikin samo hanyoyin kare muradin makiyaya ne kuma dududu a zamanin yau makiyaya da ke yawo a dazukan ba su fi ƙarfin a kidaya su a wuni daya ba rankatakaf. Fulani da ke zaune a gari da na ƙauyuka da ke da gonaki da shagunan kasuwanci kamar sauran jama’a su ne su ka fi yawa. Illar hoton Fulani a wajen Gwarawa ita ce wadannan makiyaya da ke dazuka inda da zarar fitina ta haɗa su da manoma na ƙauyuka maimakon a ce MANOMA da Makiyaya FARMERS and HERDERS sai kawai a rubuta FULANI kuma ‘yan jaridar Kudu su ka fara wannan kafin Hausawan bogi na basaja su shigo ta soshiyal midiya. A nan wasu na cewa ai na cikin gari na mara mu su baya, duk wannan maƙarƙashiya ce don kunna wutar ƙabilancin da a ke tsarawa don wargaza ƙarfin Arewa a siyasance da tattalin arziki.
Kamar yadda a ke da ƙungiyar MAHAUTA mai sarkin Fawa, kungiyar wanzamai, masunta, maƙera, manoma, dukawa da ke alaka da sana’a, hakanan makiyaya su ke kuma duk wanda ya dau bindiga ya koma daji ya na sace mutane da kisan gilla sunansa a hukumance ɗan ta’adda. Duk wanda ya dubi wata ƙabila kakaf ya yi amfani da sunanta ga ta’addanci to azzalumi ne.
Na ga wasu sun ja hankalina da duba rantsuwa da shugaban gungun karyar Hausa zalla ya yi wai da Alkur’ani don ba da kariya ga haramtacciyar turba da ya dauka ta kwangilar yaƙi da musulunci, Hausawa da Arewa. Akwai wani sullutun yaro da ya ƙalubalance ni da wai ni ma na yi irin wannan rantsuwa kan tabbatar da kwangilar nan. Ba ni da lokacin martani ga yara marar sa kunya.
Ga abubuwa 7 da zan yi sharhi ko tsokaci a kai kan faifan bidiyon:
1. Babu inda shugaban gungun nan ya ce ya rantse da Alkur’ani ko a gargajiyance don irin wannan rantsuwar ma ba ta samo asali daga tushe ba; ya ce Alkur’ani ya ci shi in kwangila ya karɓo kazalika in ba ya shirga karya. Misali ya rantse cewa Alkur’ani ya ci shi in karya ya tabka a kai na cewa an kore ni daga aiki a ɓOA. Wallahi in ya yi haka zai yabawa aya zaƙi.
2. Mun ga ya yi ta jijjiga Alkur’ani kamar littafin Iliya ɗan Mai ƙarfi ba girmamawa ko ta miskala zarratin don da alamu ba ma layinsa ba ne basaja ce kawai.
3. Maimakon ya tsaya kan batun kwangila sai ya shiga babin wai a na kore samuwar Hausawa ko a na kashe Hausawa da sauran bayanan da ba su da alaƙa da rantsuwa ma balle har ya kai ga neman wulakanta Alkur’ani ta hanyar jijjiga shi da buɗe shafukan war-war-war tamkar fallen yadin shaddar wa-gambari.
4. Ita wannan aya ta 61 ta Suratu Al-Imran na magana ne kan kiristocin Najran wadanda su ka karyata matsayin Annabi Isa na mutum kuma Annabin Allah kamar yadda ya zo a Alkur’ani. A wajensu Isa Alaihis salam dan Allah ne. Sun ƙalubalanci wahayin da a ka yi wa Manzon Allah mai tsira da aminci kan kasancewar Annabi Isa manzo ne na Allah amma sam ba dan Allah ba ne. A nan Allah ya umurci yin mubahala da waɗannan kiristoci cewa Musulmi su fito da ‘ya’yansu, matansu da ma kawunansu hakanan su ma kiristoci su yi irin wannan fita sai a yi addu’ar la’ana mai zafi ta neman Allah ya tsinewa duk mai karya. To shi shugaban wannan gungun Kiristoci ‘yan kungiyarsa zai kira a yi wannan la’ana ko ya na da membobi Musulmi ne? Shin mubahalar tsakanin Musulmi da musulmi za a yi ko tsakanin musulmi da Kirista? Ina membobin ƙungiyarsa masu rufeffen shafi da sunayen karya masu wuni su na la’antar Shehu Mujaddadi da malaman Musulunci, shin za su bayyana a yi mubahalar da su ko su sojojinsa na ɓoye don aikin aibanta mutanen kirki?.
5. Shugaban gungu ya ce kar a damu da tajwidinsa lokacin karanta ayar, shin wa ya tambaye shi batun tajwidi ma a nan? Shi ya yi karatunsa kuma ya tsargu da karatun don bai iya ba. Ba ma tajwidi ne damuwar ba, a a kafa hujja da ayar wajen jijjiga Alkur’ani da ya yi ba tare da sanin dalilin saukar ayar ba da muhallin da ta ke aiki.
6. Mai ya sa shugaban gungu bai rantse cewa Alkur’ani ya ci shi in shi ba Bahaushe ba ne. Duk nazari na nuna wannan mutumin ba Bahaushe ba ne daga yadda tarbiyyar maganarsa ta ke da furucin harshensa. Mu na son ya fito karara ya yi bayanin nasabarsa da yadda ya zama Bahaushe da a takaice irin gudunmawar da ya ba wa harshen Hausa waje da ƙabilanci a rayuwarsa kakaf.
7. Shin mai ya sa ya na ganin ‘yan gungunsa na cin zarafin mutane da jifar su da zama ‘yan zina da kazafi iri-iri amma bai taɓa tsawatawa ba? Mai ya sa bayan muhawararsa da Farfesa Abubakar Usman Ribah ya bar yaransa na zayyana Farfesa da na kwali da miyagun kalmomi amma bai taba tsawatawa ba? Wa zai ɓata lokacinsa ya yi muhawara da shi alhali ga ɗabi’ar gungunsa na cin mutunci da raina manya.
KAMMALAWA
Wannan rantsuwa sam ba ta yi ba kuma ba buƙatar kafa hujja da aya ta 61 ta Al-Imran don ba ta da alaka da abun da ya aikata. Kazalika ya fara karanta ayar ba TA’AWUZI ba BASMALA don ba ladabin hakan. Akwai kalubalen ya sake daga Alkur’ani ya rantse cewa ƙabilanci halal ne. Ba ma bukatar hujjar wai Bahaushe koya ma sa ƙabilanci a ka yi. Waye Bahaushen da su ke magana a kai? A dukkan matakai Bahaushe ke mulkin kansa da tsara duk abun da ya ke buƙata a rayuwarsa koma bayan Hausawan bogi da ke ɓoye kansu don samun damar surfa ashar da kunna fitinar yaƙin basasa na ƙabilanci.
