Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An ayyana jihohin Jigawa, Kano da Katsina a matsayin waɗanda suka fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yayin da asusun tallafa wa ƙananan yara (UNICEF) ke jaddada buƙatar tallafa wa ilimin yara daga tushe.
A cewar UNICEF, Nijeriya na da yara miliyan 18.3 da ba sa zuwa makaranta a faɗin duniya.
Jami’ar tuntuɓa na UNICEF a Kano, Aisha Abdullahi, ce ta bayyana hakan a yayin wata ganawa ta kwana biyu na ‘yan jaridu daga jihohin Jigawa da Kano da Katsina.
A yayin da take gabatar da jawabinta jan ginshiƙin koyo da bunƙasa sana’o’in hannu na zamani, ta ce, jihohin kawai suna da kaso 30% na yawan yaran da ba sa zuwa makaranta sakamakon talauci da matsalar tsaro da al’ada da rashin makarantu masu kyau.
Aisha ta jaddada cewa shirin Kula da Yara a Matakin Farko da Cigaban Ilimi (ECCDE) na samar da dabaru da kawo mafitar warware matsaloli mai dogon zango wanda ka iya hana yara daina zuwa makaranta tun kafin ma su shiga makarantar.
Ta jaddada cewa magance irin waɗannan matsaloli na buƙatar sauya salo daga jiran matsala ta farko a ɗau mataki zuwa salon amfani da dabarun magance faruwar matsalolin kafin su afku, musamman ta hanyar samar da ginshiƙin ƙarfafa ilimi a matakin farko.
“Samun ilimi a matakin farko ba iya kaɗai ginshiƙi ba ne, wata hanya ce ta rage yawan yaran da ba sa zuwa marakaranta,” Aisha ta faɗa.
A cewarta, ECCDE shiri ne da ya mayar da hankali kan yara daga haihuwa zuwa shekara 5 ta hanyar samar da tsarin bunƙasa ƙwaƙwalwa da da dabarun zamantakewa da ake buƙata wajen samun nasara a ɓangaren ilimi.
Ta kuma ce yaran da suka samu ilimi daga tushe sun fi samun damar shiga makaranta da tsayawa ganin sun kammala karatunsu a yayin da yaran da ba su samu irin wannan dama ake ganin akwai yuwuwar su gujewa zuwa makaranta.
Aisha ta ce bincike ya nuna cewa kusan kaso 90 na bunƙasar ƙwaƙwalwa na faruwa ne kafin cika shekara 5 da haihuwa wanda mataki ne mai muhimmanci wajen cusa wa yaro ɗabi’ar koyo.
Duk da wannan tsari da ya tanadi samun ilimi na shekara ɗaya kafin shiga firamare, ta ce yara da dama ba sa samun wannan dama musamman a yankunan karkara.
Ta ce a wuraren da suke da cibiyoyin ECCDE a kan samu kaso 40 na yuwuwar samun yaran da za su shiga firamare tare da ci gaba da zuwa makaranta.
ƙwararriya kan harkokin UNICEF ta ce wannan mataki na da muhimmanci wajen bunƙasa ilimin yara, musamman yara mata wanda ke rage yawan auren wuri a yayin da shigo da iyaye cikin al’amuran ‘ya’yansu.
Sai dai masu ruwa da tsaki a wurin taron, sun nuna damuwa game da rashin shigar iyayen cikin harkokin ilimin ‘ya’yansu inda kasa da kaso 15% ne suke sa hannu a cikin karatun yaransu a faɗin Arewa.
Sun ce sa hannun iyaye maza abu ne da ka iya rage ywan yaran da ba sa zuwa makaranta da kaso 50 idan aka yi la’akari da tasirin iyaye maza wajen yanke hukunci a zamantakewar aure da wayar da kan al’umma da kula da harkokin ibada da tsare-tsare da suke cike giɓin mu’amala tsakanin uba da ‘ya’yansa.
Duk da irin waɗannan matakai, waɗanda suka halarci taron sun nuna cewa akwai buƙatar yin doka da faɗaɗa shirin ECCDE a dukkan makarantun firamare da ware kuɗi na aƙalla kaso 5 daga kasafin kuɗin domin ilimi daga tushe da horas da ƙarin malamai da cusa tsarin koyarwa ta yau da kullum da ilimin addini cikin tsarin.
Sun ce zuba jari domin ƙarfafa ilimin ƙananan yara a matakin farko yadda ya kamata zai taimaka wajen samar da ilimi mai inganci da magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
