Cikar AKCILS shekaru 50: Abba Bichi da Farfesa Ibrahim sun samu lambar yabo kan tallafin ilimi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci da ke Kano, wato Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies (AKCILS), ƙarƙashin jagorancin Farfesa Balarabe Jakada, ta ba Hon. Abba Bichi, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi a Abuja, kyautar lambar yabo tare da wasu mutane bisa tallafin ilimi da suke bayarwa.

An bayar da lambar yabon ne a yayin bikin cikar kwalejin shekaru 50 da kafuwa, wanda aka gudanar a harabar makarantar a makon da ya gabata.

A jawabinsa, wanda ya karɓi kyautar a madadin Hon. Abba Bichi, mai ba shi shawara kan harkokin ilimi, Farfesa Ibrahim Habib, ya bayyana cewa Abba Bichi ya zama ginshiƙin tallafin ilimi, domin a duk shekara Allah kaɗai ya san adadin miliyoyin da yake kashewa wajen tallafawa ɗalibai, ba wai na asalin Bichi kaɗai ba. Ya ce wannan ne ya sa AKCILS ta yi bincike kafin ba shi wannan lambar yabo.

Shi ma Alhaji Ibrahim, wanda ɗan kasuwa ne kuma ya yi suna wajen tallafa wa bunƙasar ilimi da sana’o’i, ya samu irin wannan karramawa daga AKCILS bisa gudunmawarsa ga al’umma. Ya yi alƙawarin ci gaba da bayar da tallafi, sannan ya ziyarci tsofaffin ɗaliban AKCILS da suka baje kolin sana’o’i daban-daban a lokacin taron, inda ya yi alƙawarin tallafa musu.

A ƙarshe, Dakta Dauda Hassan, shugaban ƙungiyar da ya jagoranci tattaunawa kan harkar tsaro a wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 50, ya yaba wa Antoni Janar da kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barrista Abdulkarim Kabiru Maude Minjibir, wanda ya jagoranci tattaunawar domin bunƙasa tsaro a matsayin gudunmawa daga bangaren shari’a.

Haka kuma ya yaba wa shugaban makarantar Farfesa Balarabe Jakada da sauran shugabanni irinsu Farfesa Garba Shehu, wanda ya shugabanci makarantar kafin zuwan Jakada, da mataimakinsa Malam Ali Tamasi, da sauran shugabanni da sarakunan al’umma daga sassa daban-daban na Kano da ma wajenta.

By ukarofi