Daga USMAN KAROFI
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna matuƙar baƙin ciki da fushi kan rasuwar tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu, wanda aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 3 ga Mayu, 2026. Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan kwanaki tara yana hannun ‘yan bindiga duk da ƙoƙarin da iyalansa suka yi na ganin an kuɓutar da shi.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce mutuwar tsohon ɗan majalisar wata babbar shaida ce ta taɓarɓarewar tsaro a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa gwamnati ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, wanda ya ce shi ne babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗorawa gwamnati.
Atiku ya ƙara da cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali, inda ya ce mutane na tafiya a manyan hanyoyi cikin tsoro yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da ƙaruwa. Ya tambayi irin fatan da talakawan ƙasa za su yi idan har tsohon ɗan majalisa ba zai tsira daga hannun masu garkuwa da mutane ba duk da matsayinsa da tasirinsa a siyasa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fito ƙarara ta bayyana matakan da take ɗauka wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa ‘yan Najeriya ba sa buƙatar ƙarin saƙonnin ta’aziyya kawai, sai dai ingantaccen shugabanci da sakamako a aikace. Haka kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da al’ummar jihar Jigawa tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matsalar tsaro a matsayin gaggawa ta ƙasa.
